Wani mai neman samun aiki a hukumar karre haddura ta kasa ta fadi ya mutu a yayin atisaye

Wani mai neman samun aiki a hukumar karre haddura ta kasa ta fadi ya mutu a yayin atisaye

An samu tsaiko a yayin da ake tantance matasa masu neman shiga aikin hukumar kare haddura ta kasa, FRSC a garin Lokaja na jahar Kogi a daidai lokacin da wani matashi dake kokarin shiga aikin ya yanke jiki ya fadi matacce.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Talata 25 ga watan Satumba, kamar yadda shugaban hukumar FRSC reshen jahar Kogi, Olusegun Martins ya tabbatar, wanda yace marashin ya rasu ne jim kadan bayan ya kammala gudun tsere na kilomita biyu.

KU KARANTA: Shugaban hukumar tsaro ta sirri ya ziyarci farfesa Yemi Osibanjo a ofishinsa

Kwamandan hukumar, Martinsa yace lamarin ya tayar musu da hankula matuka sakamakon basu taba zaton mutuwa matashin zai yi ba, tunda har sai daya cire lambarsa daga wuyansa kafin ya fadi, daga nan kuma aka garzaya da shi asibitin dake barikin Magumeri.

Sai dai kwamandan yace matashin bai wuce mintuna Talatin ba a asibitin yace ga garinku nan, duk da haka kwamandan yace mutuwar matashin ba zai sa su soke gudanar da wannan aikin tantancewa ba.

Daga karshe kwamanda Olusegun Martinsa ya mika ta’aziyyarsa a madadin hukumar kare haddura ta kasa ga yan uwa da iyalan mamacin da bai bayyana sunansa ba.

A ranar Litinin 24 ga watan Satumba ne hukumar kare haddura ta kasa ta fara aikin tantance matasa masu sha’awar shiga aikinnasu, inda aikin tantancewa ya kunshi duba lafiyar masu nema shiga, tabbatar da sahihancin takardunsu da kuma gudun yada kanin wani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel