Na fitar da tsammanin zabe na adalci a gwamnatin Buhari - Dan takarar PDP

Na fitar da tsammanin zabe na adalci a gwamnatin Buhari - Dan takarar PDP

Wanda ya kafa Jami'ar Baza da ke Abuja kuma daya daga cikin masu neman takarar shugabancin kasa a PDP, Dr Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa babu alamun shugaba Muhammadu Buhari zai gudanar da zabe mai inganci da adalci duba da yadda ya ke tafiyar da harkokin kasar.

A wata hira da ya yi da wani dan jarida mai suna Leo Sobechi, Dr Datti Baba-Ahmed ya ce abu mai wuya ne shugaba Buhari ya iya gudanar da sahihiyar zabe da mutane za su gamsu da ita amma dai ya zama dole a yi zaben saboda haka doka ya tanada.

Na fitar da tsammanin zabe na adalci a gwamnatin Buhari - Dan takarar PDP

Na fitar da tsammanin zabe na adalci a gwamnatin Buhari - Dan takarar PDP
Source: Twitter

Datti Ahmed ya kuma ce babu wata cigaba da aka samu wajen kyautata rayuwar al'umma inda ya bayar da misalin yadda kayayakin masarufi duk su kayi tsada kuma hakan ya jefa talakawa cikin halin ha'ula'i.

DUBA WANNAN: Wani bankin bogi ya yi awon gaba da N27bn na jama'a a Cross Rivers

Dan takarar na PDP ya yi ikirarin cewa lokaci na zuwa da al'umma za su gane cewa ya fi shugaba Muhammadu Buhari nagarta inda ya ce wasu 'yan siyasar kawai suna rudan talakawa ne saboda wasu daga cikin mutanen ba su iya banbance mai fada musu gaskiya da akasin hakan.

Datti ya ce muddin aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya abubuwan da zai fara aiwatarwa sune hadin kan kasa, karfafa darajar Naira da tattalin arzikin kasa kana ya kawo karshen kashe-kashen da akeyi a wasu sassan kasar.

Daga karshe ya ce bashi da wata matsalar rashawa ko cin hanci saboda bai taba rike wani mukamin siyasa ko gwamnati ba a baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel