Daukar Aiki: Ba za mu dauki wadanda ba su cika sharudda da Ka'aidojin mu ba - FRSC

Daukar Aiki: Ba za mu dauki wadanda ba su cika sharudda da Ka'aidojin mu ba - FRSC

A yayin da hukumar kula da manyan hanyoyi ta FRSC (Federal Safety of Nigeria) ke ci gaba da tantance manema samun aikinta a dukkanin jihohin dake fadin kasar nan, ta kuma bayyana wanda kada ma su rai da ba za ta bai wa aikin ba.

Shugaban wannan hukuma, Mista Boboye Oyeyemi, ya bayyana cewa ga masu zane ko kuma rashin lafiyar gabbai musamman na kafafu ba za su samu aikinta ba domin kuwa za ta yi watsi da su a yayin tantancewa.

Oyeyemi ya bayyana hakan ga manema labarai yayin ziyarar gani da ido da ya kai wajen tantance manema aikin a Barikin sojin kasa na Ikeja dake jihar Legas a ranar Talatar da ta gabata.

A yayin ziyarar ta sa Mista Oyeyemi ya bayyana cewa, hukumar ba za ta bayar da aikin ga marasa lafiyar gabbai musamman na kafafu da idanu da kuma masu zane a jikin su da a turance ake kiransa Tattoo.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Mista Oyeyemi ya bayar da dalilin sa kan cewa ga dukkanin kowane nau'in aiki na damara, ana bukatar mai cikakkiyar lafiyar gabbai da zai iya daukan wani lokaci mai tsayin gaske a tafe ko a tsaye kyam.

Kazalika hukumar ba za ta dauki Mata masu juna biyu ba ko wadanda ke da igiyar aure rataye a wuyansu bisa tanadin ka'idar kowace hukumar aikin damara kamar yadda Mista Oyeyemi ya bayyana.

KARANTA KUMA: Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wani Yaro dan shekara 10 a jihar Kano

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu hukumar na ci gaba da tantance manema aikin kan tsari da ta fara gudanarwa a ranar Litinin din da ta gabata cikin dukkanin jihohi dake fadin kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, manema aikin hukumar ta FRSC daga jihohin Kaduna, Benuwe, Legas, Enugu, Oyo da kuma babban birnin kasar nan na tarayya sun dara na sauran jihohin kasar nan ta fuskar adadi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel