Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wani Yaro dan shekara 10 a jihar Kano

Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wani Yaro dan shekara 10 a jihar Kano

Tsautsayi da Hausawa kan ce ba ya wuce ranarsa ya afkawa wani Yaro dan shekara 10 a gida mai lamba 44 dake unguwar Sabon Gari ta jihar Kano, Ifeanyi Ogbodo, wanda wutar lantarki da raba shi da ransa daya tallin tal yayin da yake kokarin sauke nauyin aike na Mahaifiyarsa.

Lamarin kamar yadda rahotanni suka bayyana ya auku ne a sanadiyar kamfanin raba wutar Lantarki na jihar, inda bayan ma'aikatansa sun kammala aikinsu a wannan gida kuma sun kyale wayoyin wutar a tsirara inda suke reto saman rufin kwano ba tare da killacewa ba.

Wannan abun al'ajabi ya auku ne a yayin da Marigayi Ifeanyi ya rike marukin kofar gidan yayin fita domin saukewa mahaifiyarsa wani aike, inda nan take wutar lantarki ta wujijjiga har sai da ya fadi kasa wanwar a sheme.

Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wani Yaro dan shekara 10 a jihar Kano

Wutar Lantarki ta salwantar da Rayuwar wani Yaro dan shekara 10 a jihar Kano
Source: Depositphotos

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, anyi gaggawar garzaya da Ifeanyi zuwa wani asibiti na kurkusa inda ba bu jimawa rai yayi ma sa halinsa.

KARANTA KUMA: Uwargida ta sheke diyar Kishiyar ta da maganin 'Kwari a jihar Neja

A yayin tuntubar kakakin kamfanin wutar raba wutar lantarki na jihar Kano, Muhammad Kandi ya bayyana cewa, a halin yanzu tuni ma'aikatansu sun dirfafi wannan gida domin aiwatar da binciken diddigi domin tabbatar da ba'asi na aukuwar wannan mummunan lamari.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaii ziyarar jaje jihar Kogi a sakamakon aukuwar ambaliyar ruwa da ta salwantar da rayukan mutane 108 tare da raba kimanin mutane fiye da 100, 000 da muhallansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel