Yanzu Yanzu: Buhari na jawabi a Majalisar Dinkin Duniya (bidiyo)

Yanzu Yanzu: Buhari na jawabi a Majalisar Dinkin Duniya (bidiyo)

A yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73. Kalli biyo yayinda shugaban kasar ke gabatar da jawabin Najeriya a gagarumin taron shugabannin Duniya.

KU KARANTA KUMA: APC ta haramtawa shugabannin jam’iyyar a Adamawa shiga zaben fidda gwani na gwamna da za’a yi a ranar Asabar

Yayinda ake ci gaba da taron, hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie ta wallafa bidion wasu yan Najeriya dake nan domin arar da muryoyinsu da goyon bayansu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) ta ce gwamnatin tarayya ba ta burge su ba bayan ta bayyana cewar ta amince da fitar da biliyan N20bn domin gyaran jami’o’in kasar nan.

Mambobin kungiyar ASUU sun bayyana cewar kamata ya yi gwamnatin tarayya ta fitar da kudin tun watan Oktoba na shekarar 2017.

ASUU ta kara cewar kamata ya yi a ce ana tattauna yadda za a cika alkawarin dake tsakaninsu gwamnatin tarayya na shekarar 2009.

A yau, Talata, ne reshen kungiyar na Legas ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin shafa masu kashin kaji ta hanyar bayyana amincewa da sakar masu kudaden.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel