Shugaban hukumar tsaro ta sirri ya ziyarci farfesa Yemi Osibanjo a ofishinsa

Shugaban hukumar tsaro ta sirri ya ziyarci farfesa Yemi Osibanjo a ofishinsa

Sabon shugaban hukumar tsaro ta sirri, DSS, Malam Yusuf Magaji Bichi ya kai ma mataimakin shugaban kasa Frafesa Yemi Osibanjo ziyarar ban girma a ofishinsa dake fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Ko a satin data gabata sai da shugaban hukumar ta DSS ya garzaya ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari dake fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, inda ya gana da Buhari, wanda itace haduwarsu ta farko a rayuwa.

KU KARANTA: Aiki ya kwana: Ka gaggauta mayar da mataimakinka kan kujerarsa – Kotu ga Gwamnan APC

Hakan ya tabbata ne a yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake gaiswa da Malam Bichi, inda ya tambayeshi “Mun taba saduwa kuwa?” sai Malam Bichi ya amsa masa da cewa “Bamu taba saduwa ba, wannan ne karo na farko.”

Sai dai a wannan ziyarar da Bichi ya kai ma Osinbajo, ya samu damar ganawa da Farfesan a ofishinsa inda suka tattauna a bayan labule, sa’annan koda manema labaru suka mamayeshi bayan kammala ganawar sai yayi gum da bakinsa, bai ce uffan ba.

A wani labarin kuma, hukumar DSS ta tabbatar da kama dogarin uwargidar shugaban kasa Aisha Buhari akan dalilin yin sibarnabayyen wasu makudan kudade, sai dai da yammacin Talata Aisha Buhari ta musanta bada umarnin kama dogarinnata.

Idan za dai a iya tunawa, shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Aisha sun tafi kasar Amurka a ranar Lahadin data gabata domin samun damar halartar taron koli na majalisar dinkin Duniya karo na 73.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel