Ku rike kudinku, bama so: ASUU ta ki karbar biliyan N20bn daga gwamnatin tarayya

Ku rike kudinku, bama so: ASUU ta ki karbar biliyan N20bn daga gwamnatin tarayya

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) ta ce gwamnatin tarayya ba ta burge su ba bayan ta bayyana cewar ta amince da fitar da biliyan N20bn domin gyaran jami’o’in kasar nan.

Mambobin kungiyar ASUU sun bayyana cewar kamata ya yi gwamnatin tarayya ta fitar da kudin tun watan Oktoba na shekarar 2017. ASUU ta kara cewar kamata ya yi a ce ana tattauna yadda za a cika alkawarin dake tsakaninsu gwamnatin tarayya na shekarar 2009.

A yau, Talata, ne reshen kungiyar na Legas ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin shafa masu kashin kaji ta hanyar bayyana amincewa da sakar masu kudaden.

A wani taro da manema labarai a jmi’ar Legas (UNILAG), shugaban ASUU na shiyyar kudu maso yamma, Farfesa Olusiji Sowande, ya bukaci gwamnatin tarayya ta rushe kwamitin sulhu dake tsakaninta da kungiyar wanda Dakta Wale Babalakin ke jagoranta.

Ku rike kudinku, bama so: ASUU ta ki karbar biliyan N20bn daga gwamnatin tarayya

Ku rike kudinku, bama so: ASUU ta ki karbar biliyan N20bn daga gwamnatin tarayya
Source: UGC

Sowande ya bayyana cewar biliyan N20bn din da gwamnatin tarayya ta fitar na daga cikin yarjejeniyar kashe tiriliyan N1.3tn domin inganta ilimin jami’a a Najeriya da kungiyar ASUU ta kulla da gwamnatin tarayya, Kazalika ya bayyana rashin jin dadinsa bisa yadda gwamnati ta gaza kasha koda biliyan N220 domin inganta jami’o’i a cikin shekara 5.

Gwamnati ba ta taba sakar mana kowanne kudi ba, dole mu sanar da jama’a wannan. Yadda gwamnati ta bayar da sanarwa na nuna tamkar ta bawa ASUU kudi ne.

DUBA WANNAN: Duba tsarin da kowacce jiha zata yi amfani da shi wajen fitar da 'yan takara a APC

“Gwamnati na tura kudi ne ga jami’o’i. Sakin biliyan N20bn din na zuwa ne bayan amincewar da gwamnati tayi na sakinsu ga jami’o’i bayan wata daya kacal a shekarar 2017. Abinda muka yi tsammani shine zuwa yanzu gwamnatin tarayya ta kasha fiye da biliyan N220 a bangaren inganta jami’o’in Najeriya,” a cewar Sowande.

Sowande ya yi gargadin cewar kwanan nan ASUU zata kara tsunduma cikin yajin aiki muddin gwamnati bat a gaggauta cika yarjejeniyar dake tsakaninsu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel