Aiki ya kwana: Ka gaggauta mayar da mataimakinka kan kujerarsa – Kotu ga Gwamnan APC

Aiki ya kwana: Ka gaggauta mayar da mataimakinka kan kujerarsa – Kotu ga Gwamnan APC

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Owerri na jahar Imo ta soke tsige mataimakin gwamnan jahar da majalisar dokokin jahar ta yi tare da hadin bakin gwamnan jahar Rochas Okorocha.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin Kotun mai shari’a Benjamin Iheaka ne ya yanke wannan hukunci a ranar Talata, 25 ga watan Satumba, inda yace haramun a tsige mataimakin gwamnan jahar Imo Eze Madumere ba tare da bin ka’ida ba.

KU KARANTA: Babbar jami’a mafi inganci a Duniya ta nada gwamnan jahar Kaduna muhimmin mukami

Aiki ya kwana: Ka gaggauta mayar da mataimakinka kan kujerarsa – Kotu ga Gwamnan APC

Rochas da Eze
Source: UGC

Alkalin yace kwamitin mutane bakwai da Alkalin Alkalan jahar Mai sharia Pascal Nnadi ya kafa don binciken mataimakin gwamnan haramtacciya ce saboda bata yi biyayya ga sashi na 185 na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen gudanar da ayyukanta ba.

Alkalin yace sai bayan kwanaki bakwai da kundin tsarin mulki ya tanadar aka kafa wannan kwamitin, don haka ta tabbatar haramtacciya, da wannan ne kuma yayi umarni ga gwamnatin jahar Imo da ta yi maza maza wajen mayar da Eze kujerarsa.

A nasa jawabin, lauyan mataimakin gwamnan, Ken Njemanze mai mukamin SAN ya gode ma Alkalin, inda ya bayyana hukuncin daya yanke a matsayin babban lamari, ya kara da cewa hukuncin zai zamo izina ga sauran yan siyasan kasar nan.

Idan za’a tuna a watan Agustan data gabata ne aka tsige Eze daga mukaminsa bayan kwamitin da Alkalin Alkalan jahar ya kafa ta kama shi da tafka wasu manyan laifuka, wannan kuma ya tunzura Eze garayawa gaban Kotu don neman hakkinsa.

Da take tsokaci game da lamarin, wata babbar lauya a jahar Imo, Blessing Iweajunwa, ta bayyana hukuncin a matsayin wanda ya cancanci yabo, don haka ta yi kira ga yan siyasa dasu dinga bi tare da amfani da duk hukuncin da Kotu ta tanadar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel