Tattalin arziki: Najeriya na iya sullubawa ta koma cikin qaqa-nika yi - CBN yayi kashedi

Tattalin arziki: Najeriya na iya sullubawa ta koma cikin qaqa-nika yi - CBN yayi kashedi

- Najeriya ta sha ama da matsin tattalin arziki a 2015-16

- CBN tace watakil a koma ruwa, duk da an dan farfado

- Najeriya ce ta daya a arziki a Afirka, ta wuce Mista da Afirka ta Kudu

Tattalin arziki: Najeriya na iya sullubawa ta koma cikin qaqa-nika yi - CBN yayi kashedi

Tattalin arziki: Najeriya na iya sullubawa ta koma cikin qaqa-nika yi - CBN yayi kashedi
Source: Getty Images

A bayan taron karshen kwatana shekara da babban bankin Najeriya ya gama da masu ruwa da tsaki a wannan mako, gwamnan bankin, Mista Godwin Emefiele, ya bayyana cewa akwai alamu na sake sullubawa cikin qangin matsi na tattalin arziki.

A bana ne fa kawai aka fito daga wancan matsin tattalin arzikin da aka shiga a 2016, wanda faduwar mai, da ma fasa bututan mai ta jawo, da kuma dakile hanyoyin wadaqa da kudaden gwamnati da shugaba Buhari yayi, inda aka tattara duk kudaden gwamnati aka rufe a asusu guda watau TSA.

Sai dai a wancan lokaci, duk kira da babban bankin yayi, abin sai da ya kai da tattalin arzikin, mafi girma a Afirka, ya durkushe.

DUBA WANNAN: 'Muna rike da hadimin Aisha Buhari' - DSS

A cewar Mista Emefiele, a kwatar farko da ta biyu ta bana, an ga raguwar tattalin arzikin da kashi 1.90 da kuma 1.50 bisa dari jerau, maimakon habaka da ake sa rai, wanda ke nufi masu hannayen jari suna baya-baya da sanya kudinsu a kasar.

Zabukan a zasu zo a badi ma dai, suna da alaka da wannan koma baya, inda wasu kan kwashe kudadensu daga kasar, zuwa suga ko mai kaaje-yazo a watan fabrairun.

Akwai ma kuma batun satar kudaden gwamnati da 'yan siyasa kanyi, domin su kashe kudi kan sake komawa wasu kujerun, wanda ka iya janyo duk dai matsi a lalitar gwamnati.

Watakil dai, samar da ayyukan yi, kulla da sabgogin bankuna kan yadda zasu bayar da lamuni, da amso su in lokaci yayi, da ma kula da yadda lalitar gwamnati ke tsiyaya ka iya kawo sauki na wani lokaci a wucin gadi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel