Hukumar DSS ta tabbatar ta tsare mai yiwa Aisha Buhari hidima, bisa zargin cin amana

Hukumar DSS ta tabbatar ta tsare mai yiwa Aisha Buhari hidima, bisa zargin cin amana

- An kama Sani na Inna ne bisa zargin yaudara da neman kudi

- DSS sun karbe shi daga hannun 'yansanda

- Harma sun bar iyalinsa ta ganshi, an bincika asusunsa da gidansa

Hukumar DSS ta tabbatar ta tsare mai yiwa Aisha Buhari hidima, bisa zargin cin amana

Hukumar DSS ta tabbatar ta tsare mai yiwa Aisha Buhari hidima, bisa zargin cin amana
Source: Depositphotos

Bayan zarginsa da aka yi cewa yana amfani da sunan mai dakin shugaba Buhari, wadda yake hidimtawa, inda wai ya tara makudan kudade da suka kai biliyan kusan ukku, yanzu DSS ta tabbatar suna tsare dashi a ofishinsu.

Sani na-Inna, yanzu haka yana amsa tambayoyi kan ko yayi amfani da kudaden jama'a a gwamnati da 'yan siyasa don arzurta kansa, zargi da ya musanta.

Ita kuma uwar gidanshugaba Buharin, ta sa a tuhume shi ne don wai akwai makarkashiya wadda ya kamata ya iyar da kudin inda aka aike shi dasu.

DUBA WANNAN: Ko Buhari da Trump zasu gamu?

Jaridar Premium Times ce ta fasa kwan, kuma tana bin kadin yadda lamarin ke gudana.

Aisha Buhari dai tana Amurka taron majalisar dinkin duniya tare da shugaba Buhari, ba'a ji daga bakinta ba ko akwai qarin haske.

DSS din, ta bar matar shi da ta ganshi, sannan kuma an bincike gidansa dake Garki a Abuja.

Babu dai wanda ya sani ko da gaske ne ana neman kudi da sunan matar shugaban kasar, ko kuma itama tana bin manyan 'yan siyasa da gwamnati dasu bata kudi ko kwangila, sai bincike ya tsananta maji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel