Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun gamsu da sake zaben Osun

Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun gamsu da sake zaben Osun

Kasar Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun nuna gamsuwar kan karashen zaben jihar Osun da aka gintse a a ranar Asabar day a gabata.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da ofisoshin jakadancin kasashen suka fitar, sun bukaci a zauna lafiya sannan kuma a gudanar zaben cikin lumana.

Kasashen dai na daga cikin hukumomin kasashen waje da suka sa ido a zaben gwamnan na jihar Osun.

Sun kuma jinjina wa jama’ar jihar Osun da hukumar zabe mai zaman kanta da kuma hukumomin tsaro kan rawar ganin da suka taka wajen ganin an yi zaben lafiya na ranar Asabar lafiya.

Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun gamsu da sake zaben Osun

Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun gamsu da sake zaben Osun
Source: Original

A korafe-korafen da suka yi game da sake zaben da INEC za ta yi, PDP da sauran manya-manyan jigata-jigatan, sun yi kira ga manyan kasahe duniya, kan yunkurin da suka ce APC ke yi na yi wa dimokradiyya zagon kasa.

KU KARANTA KUMA: Sanata Shehu Sani ya gargadi shugaban kasa Buhari akan sayar da kadarorin Nigeria

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta zargi jam’iyyar adawa ta PDP da yunkurin yin magudi a zaben raba gardama da za a yi ranar Alhamis a jihar Osun, APC ta ce PDP na buga katunan zabe na bogi ta hanyar yin amfani da sahihan bayanan dake kan katin masu zabe.

APC ta bayyana hakan ne ga Legit.ng ta hanyar wani jawabi da sakatarenta na yada labarai, Mista Yekini Nabena, ya fitar.

Nabena ya bayyana cewar APC ta tabbatar da hakan ta hanyar samun sahihan bayanan daga mambobinta dake sassan jihar Osun da za a maimaita zaben gwamna ranar Alhamis mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel