Zagaye na biyu: APC ta zakulo wani algus da PDP ke shiryawa a jihar Osun

Zagaye na biyu: APC ta zakulo wani algus da PDP ke shiryawa a jihar Osun

- Ana cigaba da musayar maganganu tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP

- APC ta zargi PDP da yin katunan zabe na bogi domin lashe zaben raba gardana da za a yi ranar Alhamis a jihar Osun

- Jam’iyyar ta APC ta shawarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta tabbatar ba a canja rajistar masu zabe ba

Jam’iyyar APC mai mulki ta zargi jam’iyyar adawa ta PDP da yunkurin yin magudi a zaben raba gardama da za a yi ranar Alhamis a jihar Osun, APC t ace PDP na buga katunan zabe na bogi ta hanyar yin amfani da sahihan bayanan dake kan katin masu zabe.

APC ta bayyana hakan ne ga Legit.ng ta hanyar wani jawabi da sakatarenta na yada labarai, Mista Yekini Nabena, ya fitar.

Nabena ya bayyana cewar APC ta tabbatar da hakan ta hanyar samun sahihan bayanan daga mambobinta dake sassan jihar Osun da za a maimaita zaben gwamna ranar Alhamis mai zuwa.

Zagaye na biyu: APC ta zakulo wani algus da PDP ke shiryawa a jihar Osun

Dan takarar PDP yayin kada kuri'a zaben ranar Asabar
Source: Original

Kazalika ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta gudanar da bincike a kan wannan zargi da kuma bukatar ta saka ido a kan rajistar masu zabe don ganin ba a canja wasu bayanai ba.

Sai dai a nata bangaren jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Osun ta ce tayi matukar girgiza bayan ta gano cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tayi mata kuri'u 4,387 daga jimillar kuri'un da ta samu a zaben gwamnan da aka yi ranar Asabar, 22 ga watan Satumba.

DUBA WANNAN: Zaben fitar da 'yan taka a APC: Duba tsarin da kowacce jiha zata yi amfani da shi

Da yake jawabi ga manema labarai a yammacin jiya, Litinin, sakataren jam'iyyar PDP na yankin kudu maso yamma, Bunmi Jenyo, ya ce INEC ta rage adadin kuri'un PDP daga mazabun Olorunda da Osogbo tare da yin aringizon kuri'un ga jam'iyyar APC.

Jenyo ya ce PDP ta gano hakan ta hanyar binciken da ta gudanar. A cewar Jenyo, bayanan dake takardar nadar sakamako (fam EC 8C) na hukumar INEC a karamar hukumar Olorunda ya nuna cewar PDP ta samu APC kuri'u 14,867 amma sai a wurin tattara sakamako aka shigar da kuri'u 16,254, an yi mata karin kuri'u 1,387.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel