Sanata Shehu Sani ya gargadi shugaban kasa Buhari akan sayar da kadarorin Nigeria

Sanata Shehu Sani ya gargadi shugaban kasa Buhari akan sayar da kadarorin Nigeria

- Cikin babbar murya, Sanata Shehu Sani ya bukaci shugaban kasa Buhari da ya dakatar da kudurin sayar da kadarorin Nigeria

- Sani ya yi ikirarin cewar sayar da kamfanonin yaa yi kama da sayar da kamfanin NEPA, inda tsiraru ke amfana yayin da talakawa ke wahala

- Legit.ng ta ruwaito maku cewa gwamnatin tarayya ta ce za ta sayar da wasu kamfanoni 10 don samun kudaden kasafin 2018

Jim kadan baya da gwamnatin tarayya ta bayyana kudurinta na sayar da wasu kamfanonin Nigeria guda 10 don harhada kudaden kasafin 2018, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yanke wannan danyen hukunci yana mai cewa wannan ba dabara mai yiyuwa bace.

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter yana mai cewa ya zama wajibi shugaba Buhari ya janye wannan kuduri nasa na sayar da kadarorin al'umma, musamman akan harhada kudaden kasafin 2018.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin tarayya za ta sayar da kamfanoni 10 na kasar don samun kudin kasafin 2018

Sanata Shehu Sani ya gargadi shugaban kasa Buhari akan sayar da kadarorin Nigeria

Sanata Shehu Sani ya gargadi shugaban kasa Buhari akan sayar da kadarorin Nigeria
Source: Twitter

Sani ya yi ikirarin cewar sayar da kamfanonin zai zama kamar dai yadda aka sayar da kamfanin da ke rarraba wutar lantarki NEPA ga 'yan kasuwa, lamarin da ke karawa wasu tsirarun mutane karfi yayin da ke durkusar da rayuwar marasa karfi da dama a kasar.

Cikin babbar murya, Sanatan ya bukaci Buhari da ya dakatar da wannan kuduri na sayar da kamfanonin.

KARANTA WANNAN: Hafsan rundunar sojin kasa TY Buratai ya gargadi jami'an soji daga sa hannu a harkokin siyasa

Joe Anichebe, daraktan kula da harkokokin kudaden jama'a na kasa, ya ce akwai yiyuwar gwamnatin tarayya ta sayar da wasu kamfanoninta guda 10 kafin karshen shekarar nan ta 2018. A cewar daraktan, kamfanonin idan aka sayar da su, za a iya samun akalla N289bn don samar da kudaden kasafin 2018.

Anichebe ya ce shirye shirye sun riga da sun yi nisa na sayar da kamfanonin, wanda suka shafi na bangaren sufurin jiragen sama da kuma inshora.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel