Hukumar kwastam ta samu kudin shiga N852m a jihar arewa cikin wata daya

Hukumar kwastam ta samu kudin shiga N852m a jihar arewa cikin wata daya

Hukumar Yaki da Fasakwabri na kasa Kwastam ta Jihohin Kaduna/Katsina sun tara kudaden shiga N852 miliyan a cikin watan Augustan wannan shekarar.

Kwamtrollar Rundunar, Oyeleke Abdulrazak ne ya bayyana hakan yayin da yake hira da manema labarai a jihar Katsina.

Ya ce kudaden da suka tara ya fi yawan adadin N342 da aka baiwa rundunar a watan na Augusta.

Hukumar Kwastam ta tara kudin shiga N852m

Hukumar Kwastam ta tara kudin shiga N852m

DUBA WANNAN: Buhari ya nada sabon shugaban hukumar NIWA

Mr Abdulrazak ya ce hukumar ta kama kayayaki 81 wanda kudin harajinsu ya tasanma N32.7 miloiyan a lokacin da akayi bita kan kudaden.

Ya ce cikin kayayakin da aka kama sun hada buhunnan shinkafar kasar waje 606, buhunnan sugar na kasar waje 239 da kuma daurin kayan gwanjo guda 73.

Saura sun hada da jarkokin man gyada 327, motoccin hawa 28, babura biyu da babban mota guda daya.

Mr Abdulrazak ya ce hukumar ta samu wannan gagarumin nasarar ne saboda kwazo da kokarin jami'an binciken sirri na hukumar da kuma hadin kan da suke samu daga sauran hukumonin tsaro na kasa.

Daga karshe ya gargadi jama'a su dena shiga harkan safarar haramtattun kayayaki inda ya ce hukumar a shirye ta ke ta taimakawa jama'a wajen gudanar da kasuwancin na kayayakin da doka ta halasta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel