Zaben Osun: Yadda INEC tayi mana kwangen kuri'u 4,387 - PDP

Zaben Osun: Yadda INEC tayi mana kwangen kuri'u 4,387 - PDP

Jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Osun ta ce tayi matukar girgiza bayan ta gano cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tayi mata kuri'u 4,387 daga jimillar kuri'un da ta samu a zaben gwamnan da aka yi ranar Asabar, 22 ga watan Satumba.

Da yake jawabi ga manema labarai a yammacin jiya, Litinin, sakataren jam'iyyar PDP na yankin kudu maso yamma, Bunmi Jenyo, ya ce INEC ta rage adadin kuri'un PDP daga mazabun Olorunda da Osogbo tare da yin aringizon kuri'un ga jam'iyyar APC. Jenyo ya ce PDP ta gano hakan ta hanyar binciken da ta gudanar.

A cewar Jenyo, bayanan dake takardar nadar sakamako (fam EC 8C) na hukumar INEC a karamar hukumar Olorunda ya nuna cewar PDP ta samu APC kuri'u 14,867 amma sai a wurin tattara sakamako aka shigar da kuri'u 16,254, an yi mata karin kuri'u 1,387.

Zaben Osun: Yadda INEC tayi mana kwangen kuri'u 4,387 - PDP

Zaben Osun: Yadda INEC tayi mana kwangen kuri'u 4,387 - PDP
Source: UGC

Kazalika, ya zargi INEC da yin irin wannan aringizon ga APC a sakamakon zaben karamar hukumar Osogbo, inda ya ce ainihin kuri'un da APC ta samu 21,479 ne amma aka shigar da cewar ta samu kuri'u 23,379.

DUBA WANNAN: Rigima: Karuwar da wani direba ya dauko ta gudu da motar maigidansa ta N5m

Jenyo ya kara da cewar INEC ta shigar da kuri'u 14,399 a matsayin na PDP daga karamar hukumar Ayedaade bayan cewar jam'iyyar ta samu kuri'u 14,599 ne daga karamar hukumar.

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewar zata tafi kotu domin neman a dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) daga maimaita zabe a wasu mazabu a zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala ranar Asabar tare da tilasta mata bayyana dan takararta a matsayin zakaran da ya lashe zaben.

A jawabin da sakatarenta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, ya fitar a jiya, Litinin, PDP ta ce an kammala zabe a dukkan mazabu da kananan hukumomin jihar Osun kuma an sanar da su, a saboda haka bata ga hujjar INEC na cewar za a je zagaye na biyu domin tabbatar da wanda ya yi nasara a zaben ba.

PDP ta kafe kan cewar dan takararta, Sanata Ademola Adeleke, ya lashe zaben bayan samun kuri’u mafi rinjaye a saboda haka ya zama wajibi hukumar INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya she zaben bisa dogaro da kwandin tsarin tsarin mulkin Najeriya da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 1999.

Bisa dogaro da wannan hujjoji, jam’iyyar PDP ta ce tana da yakinin kotu zata hana INEC gudanar da sabon zaben tare da tilasta mata bayyana dan takarar ta, Sanata Ademola Adeleke, a matsayin zakaran day a lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel