Hukumar Hisba za ta fara kamen karuwai a jihar Jigawa

Hukumar Hisba za ta fara kamen karuwai a jihar Jigawa

Hukumar Hisba reshen jihar Jigawa, ta ja kunnen karuwai da ke tambele a jihar da su daina karuwanci ko kuma a gaggauta kama su sannan a yanke masu hukunci.

Kwamandan Hisba na jihar Abubakar Maisoma ne ya yi wannan kakkausan gargadin a ranar Lahadi a Kirikasamma, yayin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya.

Ya bayyana cewa addinin musulunci ya haramta karuwanci, haka kuma dokar jihar Jigawa ita ma ta haramta shi a jihar.

Hukumar Hisba za ta fara kamen karuwai a jihar Jigawa

Hukumar Hisba za ta fara kamen karuwai a jihar Jigawa
Source: Depositphotos

Daga nan sai Maisoma ya ce hukumar sa ta aika da takardar gargadin daina sana’ar a wasu gidajen karuwai a garuruwan Kirikasamma, Kwanduk, Tasheguwa, Madaci da Marma.

Ya ce an rubuta takardar ne bayan tashi daga wani taron kwamitin tsaro na jihar, wanda ya amince da fara kai farmaki a gidajen karuwan da ke fadin jihar.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Bindow ya bayyana abinda sake zabensa zai haifar a jihar Adamawa

Taron inji shi ya hada jami’an Hisba, ‘yan sanda, SSS da sauran jami’an tsaro.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa yan Hisba sun sanar da cafke wasu yan mata a cikin birnin kano bisa lafin rashin ɗa'a.

Kamfanin dillacin labarai ta kasa (NAN) ya bayyana cewa dukkanin wani laifi na rashin ɗa'a ya saɓawa dokar shari'a a jihar Kano, wanda shi ne maƙasudin da yasa hukumar ta yi awon-gaba dasu.

Hukumar Hisbah ta cafke wasu 'yan mata 5 bisa laifin baɗala Hukumar Hisbah ta cafke wasu 'yan mata 5 bisa laifin baɗala Kakakin hukumar ta hisbah Malam Adamu Yahaya ya bayyanawa NAN cewa hukumar ta cafke 'yan matan ne a wani sumamane na musamman da suka kai a unguwar Ɗanbare dake karamar hukumar Gwale da misalin karfe 9 na dare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel