Gwamna Bindow ya bayyana abinda sake zabensa zai haifar a jihar Adamawa

Gwamna Bindow ya bayyana abinda sake zabensa zai haifar a jihar Adamawa

A ranar yau ta Talata gwamnan jihar Adamawa dake yankin Arewa maso Gabashin kasat nan ta Najeriya, Muhammad Jibrilla Bindow, ya bayyana tasirin da sake zabensa a yayin babban zabe na 2019 zai haifar a siyasar jiharsa.

Gwamna Bindow kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito cewa, sake zabensa karo na biyu a yayin zaben 2019 zai kawo karshen duk wata siyasa ta Ubangida a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabansa ga wakilan da kuma jiga-jigan jam'iyyarsa ta APC reshen mazabar jihar ta Tsakiya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, mazabar Sanatan jihar Adamawa ta Tsakiya ta kunshi kananan hukumomi 7 da suka hadar da; Hong, Gombi, Song, Girel, Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da kuma Fofore.

Gwamna Bindow ya bayyana abinda sake zabensa zai haifar a jihar Adamawa

Gwamna Bindow ya bayyana abinda sake zabensa zai haifar a jihar Adamawa
Source: Depositphotos

A yayin da Gwamnan ke ci gaba da gabatar da jawabansa, ya hikaito yadda wannan wakilai na jam'iyyar ba tare da sabawa juna ba suka tsayar da shi a matsayin gwanin takara na jam'iyyar ba tare da tasirin kudi ko kwadayi ga wani abin duniya.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya kai ziyarar jaje jihar Kogi da ambaliyar ruwa ta kassara Mutane 108

A cewarsa, ya na kyautata zaton wannan wakilai za su sake kwatanta abinda suka aikata a shekarar 2014 da ta gabata yayin zaben da ya fidda gwani na jam'iyyar da za a gudanar a bana.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar, ya shiga wata ganawar sirrance cikin gaggawa tare da shugaban hukumar zabe na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu dangane da zaben gwamnan jihar Osun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel