Ziyarar Amurka: Ko za'a sake haduwa shugaba Trump da Buhari?

Ziyarar Amurka: Ko za'a sake haduwa shugaba Trump da Buhari?

- An jiyo shugaban Amurka wai yana zunden takwaransa na Najeriya kan ziyarar da yayi

- Rahotannin sun nuna shugaban Amurkas ya raina tunanin da kuzarin Buhari

- An jiyo fadar shugaban kasa ta Aso Rock tana kushe masu kawo rahoton da cewa 'yan gutsuri tsoma ne

Ziyarar Amurka: Ko za'a sake haduwa shugaba Trump da Buhari?

Ziyarar Amurka: Ko za'a sake haduwa shugaba Trump da Buhari?
Source: UGC

Tun bayan da rahotannin gulma suka fito, kan cewa wai shugaban Amurka yace bai so a sake hada shi da shugaban Najeriya Buhari, kan wai shugaban na Najeriya bashi da kuzari da karsashi, yanzu dai shugaba Buharin ya sake garzawa Amurkas taro.

A taron majalisar dinkin duniyar dai, kowanne shugaban kasa zai halarta, kuma ana zama a gefe da shugabanni a bayan fage don shiga yarjeniyoyi da ma sulhu, ko diflomasiyya tsakanin kasashen da jama'unsu.

DUBA WANNAN: Makarantun Amurka na neman dalibai daga Najeriya

Sai dai ba'a san ko shugaba Buhari na Najeriya, a 'yan tawagarsa zasu so su sake haduwa da shugaban Amurkar ba, ba kuma a san ko na Amurkan suma borin kunya zai barsu su zauna da na Najeriyar ba, bayan katobaras da ta tsiyayo daga bakin jaridu daga Ingila.

Martanin Najeriya a wancan rahoto dai, shine cewa labarin na gulma ne, tunda a hukumance shugaban na Amurka bai furta ba, to baza ayi aiki dashi ba.

Sai dai kuma ta ciki na ciki, a gefe guda, kowa yasan irin katobaras da shugaban Amurkan kan tafka, kuma wannan kadan da aikinsa ne.

Ko za'a hadu da Sahoro da Sahorami a wannan ziyarar, sai baba ta gani...

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel