Osinbajo ya kai ziyarar jaje jihar Kogi da ambaliyar ruwa ta kassara Mutane 108

Osinbajo ya kai ziyarar jaje jihar Kogi da ambaliyar ruwa ta kassara Mutane 108

Mun samu cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya kai ziyarar jaje can jihar Kogi dake Arewa ta Tsayi a Najeriya sakamakon ambaliyar ruwa da ta kassara kimanin rayuka 108 tare da raba mutane 141, 369 da muhallansu.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, mataimakin shugaban kasar ya sha alwashin tallafi na agaji da gwamnatin tarayya za ta bai wa al'umma da yankunan jihar da wannan annoba ta afkawa.

Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan alkawari a yayin da ya ziyarci wani sansanin 'yan gudun hijira na St. Luke's dake garin Koton-Karfe a jihar ta Kogi.

Rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin shugaban kasar ya kai ziyararsa ta jajantawa tare da Gwamnan jihar, Yahaha Bello, inda suka kewaye yankuna mafi fuskantar ta'adi na wannan annobar musamman na karamar hukumar Ibaji ta jihar.

Osinbajo ya kai ziyarar jaje jihar Kogi da ambaliyar ruwa ta kassara Mutane 108

Osinbajo ya kai ziyarar jaje jihar Kogi da ambaliyar ruwa ta kassara Mutane 108
Source: UGC

A yayin haka cibiyarar bayar da agaji na gaggawa ta NEMA, ta bayar da rahoton cewa a halin yanzu akwai kimanin mutane 441, 251 da ambaliyar ruwa ta kassara cikin kananan hukumomi 50 dake fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: Tashar Jirgin Kasa ta garin Abuja ta fara aikin jigila a ranar Litinin

Legit.ng da sanadin kakakin cibiyar NEMA, Sanni Datti ta fahimci cewa, aukuwar ambaliyar ruwa a jihar Kogi ta salwantar da rayukan Mutane 108 tare da jikkatar mutane 192, yayin da 141, 369 suka rasa muhallansu.

Kazalika kididdigar bincike ta bayyana cewa, a halin yanzu ba bu wata jiha mafi shiga cikin yanayi na damuwa sakamakon girman ta'adi a sanadiyar aukuwar ambaliyar ruwa a jihar Kogi da ta yiwa ta sauran fintinkau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel