Gwamnatin tarayya za ta sayar da kamfanoni 10 na kasar don samun kudin kasafin 2018

Gwamnatin tarayya za ta sayar da kamfanoni 10 na kasar don samun kudin kasafin 2018

- Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta sayar da kwamfanoni 10 da kudinsu ya kai akalla N289bn

- Za ta sayar da kamfanonin ne a kokarinta na samar da kudaden kasafin 2018

- Tuni shirye shirye suka yi nisa na sayar da kamfanonin, wanda suka shafi na bangaren sufurin jiragen sama da kuma inshora

Joe Anichebe, daraktan kula da harkokokin kudaden jama'a na kasa, ya ce akwai yiyuwar gwamnatin tarayya ta sayar da wasu kamfanoninta guda 10 kafin karshen shekarar nan ta 2018. A cewar daraktan, kamfanonin idan aka sayar da su, za a iya samun akalla N289bn don samar da kudaden kasafin 2018.

Anichebe ya ce shirye shirye sun riga da sun yi nisa na sayar da kamfanonin, wanda suka shafi na bangaren sufurin jiragen sama da kuma inshora.

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanonin da za a fara sayarwa sun hada da kamfanin inshora na Nicon Insurance Ltd da kuma kamfanin sufurin jiragen sama na Skyway Aviatio Handling Co., wanda daraktan ya ce za a sayar da su "a wannan watan ko farkon wata na gaba" ta hanyar cinikin bainar jama'a.

KARANTA WANNAN: Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun

Gwamnatin Buhari za ta sayar da kamfanoni 10 na kasar don samun kudin kasafin 2018

Gwamnatin Buhari za ta sayar da kamfanoni 10 na kasar don samun kudin kasafin 2018
Source: UGC

Ita Enang, babban mai tallafawa shugaban kasa ta fuskar harkokin majalisun dokoki na kasar, ya ce kaso mafi tsoka daga kasafin 2018 zai samu ne daga basussukan da gwamnatin tarayya za ta ciyo.

"Shugaban kasa ya sa hannu akan kasafin kudin. A yanzu haka muna kan aiki don ganin an tabbatar da kasafin. Muna kan duba hanyoyin da za mu samar da kudaden kasafin, sai dai mafi tsoka na kasafin zai samu ne ta hanyar ciyo basussuka, saboda haka muna kan bin matakai masu kyau da za su haifar da d'a mai ido kafin mu gabatar da shi gaban majalisa," a cewar Enang.

A baya baya dai babban bankin Nigeria CBN ya biya N12.4bn don siyen kaso 21 na kamfanin NSPMC (Nigeria Security Printing and Minting Company) a turance.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel