APC a Niger ta fara gudanar da kamfen na gida-gida

APC a Niger ta fara gudanar da kamfen na gida-gida

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Niger ta fara gudanar da kamfen na gida-gida da na cikin gari domin inganta shirye-shiryen jam’iyyar a jihar.

Alhaji Mohammed Imam, shugaban jam’iyyar a jihar ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Niger a ranar Talata, 25 ga watan Satumba.

Ya bayyana cewa kamfen din da ziyarce-ziyarce ya fara ne daga mazabu zuwa yankuna, kananan hukumomi, da kuma bangarorin jihar.

APC a Niger ta fara gudanar da kamfen na gida-gida

APC a Niger ta fara gudanar da kamfen na gida-gida
Source: Depositphotos

Jigon na APC ya bayyana cewa shirin zai ba jam’iyyar damar sanar da magoya bayanta kan yadda aka tafiyar da kudaden kasar don samar da yancin damokardiya ga al’umma.

Imam ya bukaci masu jefa kuri’u a jihar da su zabi ci gaba domin ci gaba da tafiya akan tafarkin chanji da zai daura jihar kan tafarkin cigaba.

KU KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ya lalata gonar shinkafa mallakar Garba Shehu a jihar Jigawa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike yayi kira ga yan Najeriya da suyi aiki da hankali wajen fatattakan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga kan mulki a 2019.

Wike yace gwamnatin APC bata tabuka wani abun arziki ba kuma ta gaza cika alkawaran zaben da ta dauka.

Da yake Magana a gidan gwamnatin Jihar Port Harcourt a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba, Wike yace ya zama dole yan Najeriya su hada kai wajen tabbatar da cewar APC ta sha kaye a zaben shekara mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel