2019: PDP ta shirya kwatar mulki daga hannun APC da karfin tuwo – Buba Galadima

2019: PDP ta shirya kwatar mulki daga hannun APC da karfin tuwo – Buba Galadima

Tsohon shugaban kungiyar sabuwar APC wato Reformed All Progressive Congress (R-APC), Buba Galadima, ya yi zargin cewa gurgurcewar tattalin arziki, rashin tsaro a wasu yankunan kasar da rashin aminci ag bangaren jam’iyyar All Progressives Congress (APC) alamu ne dake nuna cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kan hanyar kwace mulki daga hannun jam’iyyar mai mulki ta karfin tuwo.

Legit.ng ta tattaro cea Galadima wanda ya kasance mamba a kwamitin tantance yan takarar wamna a PDP a kudu maso kudu, ya bayyana cewa jajircewa, rashin kabilanci na shugabanxi irin an Gwamna Sariake Dickson da sauran gwamnonin PDP a fadin kasar ya nuna cewa ta shirya kai kasar ga tuhun inganci da ci gaba.

2019: PDP ta shirya kwatar mulki daga hannun APC da karfin tuwo – Buba Galadima

2019: PDP ta shirya kwatar mulki daga hannun APC da karfin tuwo – Buba Galadima
Source: Depositphotos

Galadima ya bayyana hakan ne a gaisuwar ta’aziyya da suka je yi ma gwamnan na jihar Bayelsa akan rashin mahaifiyarsa da yayi a kwanakin baya.

Ya yaba ma gwamna Dickson akan tarin kokari da yake a jiharsa dama kasa baki daya, inda ya bayyana marigayiya mahaifiyar gwamnan a matsayin jarumar mata tunda ta iya renon mutun kamar gwamnan.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta halarci taron matan shugabannin Afrika (hotuna)

A baya Legit.ng ta rahoto jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Niger ta fara gudanar da kamfen na gida-gida da na cikin gari domin inganta shirye-shiryen jam’iyyar a jihar.

Alhaji Mohammed Imam, shugaban jam’iyyar a jihar ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Niger a ranar Talata, 25 ga watan Satumba.

Ya bayyana cewa kamfen din da ziyarce-ziyarce ya fara ne daga mazabu zuwa yankuna, kananan hukumomi, da kuma bangarorin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel