Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun

Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun

- Manyan kasashen duniya da ke gudanar da ayyukansu a Nigeria sun tsoma nasu bakin a sake zaben wasu sassa na jihar ta Osun

- Jakadun hadakar kungiyar kasashen turai, kasar Burtaniya da Amurka sun yaba bisa yadda aka gudanar da zaben a ranar Asabar

- Sunyi hadaka wajen kira ga jama'a da su nuna dattako da kuma kauracewa saye da sayar da kuri'u a yayin gudanar da zaben zagaye na biyu

Bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana matsayarta na sake gudanar da wani zaben a wasu sassa na jihar Osun, bayan da aka kammala zaben gwamnan jihar a ranar Asabar, tare da bayyana sakamako a ranar Litinin, manyan kasashen duniya da ke gudanar da ayyukansu a Nigeria sun tsoma nasu bakin a sake zaben wasu sassa na jihar ta Osun.

Jakadun hadakar kungiyar kasashen turai, kasar Burtaniya da Amurka sun yaba bisa yadda aka gudanar da zaben a ranar Asabar, a lokaci daya kuma suna kira ga al'ummar jihar dama kasar baki daya, da su wanzar da zaman lafiya da bin doka a lokacin da za a gudanar da zaben karo na biyu.

KARANTA WANNAN: Kungiyar kwadago za ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani ranar Alhamis

Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun

Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun
Source: Original

Zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar, INEC ta bayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba biyo bayan gaza gudanar da zabe a wasu rumfunan zabe da ke kananan hukumo 3 na jihar.

Dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Boyega Oyetola da kuma takwaransa na jam'iyyar PDP, Yekeen Adeleke na a halin kunnen doki da tseriyar kuri'u 353 a tsakaninsu.

A cikin wata sanarwar hadin guiwa daga sashen watsa labarai na ofishin jakadancin Amurka da ke nan Nigeria, kasashen guda biyu sunyi hadaka wajen kira ga jama'a da su nuna dattako da kuma kauracewa saye da sayar da kuri'u.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel