Wike ya bukaci yan Najeriya da su fatattaki APC a 2019

Wike ya bukaci yan Najeriya da su fatattaki APC a 2019

- Gwamna Nyesom Wike yayi kira ga yan Najeriya da suyi aiki da hankali wajen fatattakan jam’iyyar APC daga mulki

- Wike yace APC bata tsinanawa yan Najeriya komai ba

- Ya ce sun gaza cika alkawaran zaben da suka daukar ma al'umman kasar

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike yayi kira ga yan Najeriya da suyi aiki da hankali wajen fatattakan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga kan mulki a 2019.

Wike yace gwamnatin APC bata tabuka wani abun arziki ba kuma ta gaza cika alkawaran zaben da ta dauka.

Wike ya bukaci yan Najeriya da su fatattaki APC a 2019

Wike ya bukaci yan Najeriya da su fatattaki APC a 2019
Source: Depositphotos

Da yake Magana a gidan gwamnatin Jihar Port Harcourt a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba, Wike yace ya zama dole yan Najeriya su hada kai wajen tabbatar da cewar APC ta sha kaye a zaben shekara mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta halarci taron matan shugabannin Afrika (hotuna)

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Wike, ya caccaki wasu yan takaran kujeran shugaban kasa daga Arewa wadanda suka nuna rashin yardansu kan shirya taron gangamin jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) a garin PortHarcourt, jihar Rivers.

Ya bayyana cewa wadannan yan takara makiya jihar Ribas ne kuma Neja Delta ga baki daya. Za’a gudanar da taron gangamin ne ranan 5 da 6 ga watan Oktoba 2018.

Duk da cewa wasu daga cikin yan takaran 13 basu da matsala da gudanar da taron a Ribas, wasu sun nuna rashin amincewansu da wannan abu.

Wike ya ce yan takaran sun fara saba alkawuransu na cewa zasu tabbatar da garambawul idan suka ci zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel