Taron Gangamin PDP: Yan takaran da basu son ayi a Ribas makiya Neja Delta ne – Wike ya caccaki yan takara daga Arewa

Taron Gangamin PDP: Yan takaran da basu son ayi a Ribas makiya Neja Delta ne – Wike ya caccaki yan takara daga Arewa

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya caccaki wasu yan takaran kujeran shugaban kasa daga Arewa wadanda suka nuna rashin yardansu kan shirya taron gangamin jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) a garin PortHarcourt, jihar Ribas.

Ya bayyana cewa wadannan yan takara makiya jihar Ribas ne kuma Neja Delta ga baki daya. Za’a gudanar da taron gangamin ne ranan 5 da 6 ga watan Oktoba 2018.

Duk da cewa wasu daga cikin yan takaran 13 basu da matsala da gudanar da taron a Ribas, wasu sun nuna rashin amincewansu da wannan abu.

Wike ya ce yan takaran sun fara saba alkawuransu na cewa zasu tabbatar da garambawul idan suka ci zabe.

Yace: “Wadanda suke nuna rashin amincewa da gudanar da taron gangamin a Fatakwal yan bakin cikin cigaban jihar Ribas da Neja Delta. Idan kana nunawa mutanen jihar da Neja Delta kiyayya a fili tun yanzu, to me zakayi idan ka zama shugaban kasa?

Ta yaya zaka fadawa mutan jihar da ka nuna karara baka son jiharsu su zabeka a zabe?”

“Wajibi ne mu hada kai, bamu bukatar rabuwar kai a yanzu. Manufarmu shine sai munci a 2019.”

Mun kawo muku rahoton cewa labarin da muke samu na nuni da cewa an samu sabani a tsakanin kwamitin zartaswa watau National Working Committee (NWC) da kuma kwamitin amintattu watau Board of Trustees (BoT) na jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya.

Sabanin dai kamar yadda muka samu bai rasa nasaba ne da wurin da ake so a gudanar babban gangamin jam'iyyar wanda a wurin ne za'a zabi dan takarar jam'iyyar da zai tunkari zaben 2019.

Legit.ng ta samu cewa a lokacin da yake rantsar da kwamitin gudanar da taron gangamin, shugaban jam'iyyar ta PDP Prince Uche Secondus ya ce a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ne za'a gudanar da gangamin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel