Wani bankin bogi ya yi awon gaba da N27bn na jama'a a Cross Rivers

Wani bankin bogi ya yi awon gaba da N27bn na jama'a a Cross Rivers

- Wani banki na bogi ya tattara kudaden mutane fiye da 13,000 ya yi awon gaba da su

- Bankin ya rika yiwa mutane alkawarin basu riba mai kauri ne idan suka saka kudadensu ya yi kwanaki 40

- Sai dai bayan wasu kwanaki, bankin ta rufe ofishinta kuma aka nemi ma'aikanta aka rasa tare da kudaden jama'a

Wani bankin bogi mai suna Micheno Multipurpose Cooperative Society, (MMCS) ya damfari a kalla mutane 13,000 inda ya arce da kudadensu har na N27 miliyan a jihar Cross Rivers.

Bankin wanda wani Michael Eke ya kafa ya yiwa abokan huldar ta alkawarin samun ribar N50,000 da duk wanda ya bude asusun ajiya da N100,000 bayan kwanaki 40, wandanda kuma suka bude ajiyar da N150,000 za su samu N300,000 bayan kwana 40.

Wani bankin bogi ya yi awon gaba da N27bn na jama'a a Cross Rivers

Wani bankin bogi ya yi awon gaba da N27bn na jama'a a Cross Rivers
Source: Twitter

An dai kafa bankin ne a Calabar a watan Yunin 2018 kuma mutane da yawa suna ta tururuwa suna bude asusun ajiya da bankin domin su amfana da garabasar da bankin ya yi alkawarin bayarwa.

DUBA WANNAN: Dan takarar APC a Kwara ya tona asirin cin hancin da Saraki ya yi masa alkawari idan ya bi shi PDP

Wasu daga cikin wandanda suka bude asusun ajiya da bankin sun ce sun tattara dukkan kudin da suka mallaka a rayuwansu ne na fanso da gratuity inda suka saka ran za su samu riba mai tsoka bayan kwana 40.

Sai dai abin mamaki shine bayan kwanaki 40 din wasu daga cikin masu ajiya sun sami wani kaso na kudadensu amma fiye da 13,000 ba su ji ko uffan ba kuma a yanzu misalin kwana 30 kenan bankin ya rufe ofishinsa an nemi su an rasa.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Ms Irne Ugbo ta ce mutane da dama da suka saka kudadensu a bankin sun shigar da kara ofishin 'yan sanda kuma a halin yanzu an fara gudanar da bincike domin gano abinda ya faru da kudadensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel