Sojojin saman Najeriya sun yi fata-fata da 'bankin' makamai na 'yan Boko Haram a Sambisa

Sojojin saman Najeriya sun yi fata-fata da 'bankin' makamai na 'yan Boko Haram a Sambisa

- Sojojin saman Najeriya sun yi fata-fata da 'bankin' makamai na 'yan Boko Haram a Sambisa

- Sun samu gagarumar nasara akan 'yan ta'addan

Jami'an sojojin saman Najeriya dake a cikin rundunar hadin gwuiwa ta Lafiya Dole dake yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan sun sanar da samun gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan a maboyar su dake a dajin Sambisa.

Sojojin saman Najeriya sun yi fata-fata da 'bankin' makamai na 'yan Boko Haram a Sambisa

Sojojin saman Najeriya sun yi fata-fata da 'bankin' makamai na 'yan Boko Haram a Sambisa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani jigo a APC ya fadi mai dagulawa Buhari lissafi a gwamnatin sa

Kamar yadda muka smu, rundunar ta bayyana cewa ta samu yin galaba akan 'yan ta'addan ne tare kuma da yin fata-fata da ma'ajiyar makaman a dajin na Sambisa dake zaman mafaka gare su.

Legit.ng ta samu cewa jami'in hulda da jama'a na jami'an kuma mai magana da yawun su, Air Commodore Ibikunle Daramola shine ya sanarwa da manema labarai hakan a hedikwatar rundunar sojin saman dake a garin Abuja, babban birnin tarayya, Abuja.

Air Commodore Ibikunle Daramola ya kara da cewa wani bincike sirri ne da jami'an su suka gudanar a sararin samaniya suka gano maboyar makaman na 'yan Boko Haram kafin daga bisani su shirya su kuma kai masu hari.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Kano mun samu cewa sun kai wata mamaya a gidan shugaban kwamitin riko na jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kano ranar Litinin din da ta gabata, 24 ga watan Satumba.

Su dai 'yan sandan kamar yadda muka samu, sun je gidan shugaban rikon ne dake a kan titin Sokoto dake garin na Kano inda suka tarwatsa 'ya'yan kwamitin da sauran magoya bayan jam'iyyar ta PDP a jihar Kano dake shirin gudanar da wani taro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel