‘Dankwambo yayi alkawarin maida karatu kyauta idan ya samu mulkin Najeriya

‘Dankwambo yayi alkawarin maida karatu kyauta idan ya samu mulkin Najeriya

- Gwamna Dankwambo yana neman maida ilmin Boko kyauta a Najeriya

- ‘Dan takarar na PDP yace a zamanin sa bai biya ko sisi wajen karatu ba

- Ibrahim Dankwambo na kokarin yi wa jama’a abin da aka yi masu a da

‘Dankwambo yayi alkawarin maida karatu kyauta idan ya samu mulkin Najeriya

‘Dankwambo zai maida karatun Boko ya zama kyauta a Najeriya
Source: Depositphotos

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Gwamnan Jihar Gombe Dr. Ibrahim Hassan ‘Dankwambo kuma ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP yayi alkawarin maida karatun Boko a Najeriya kyauta idan ya zama Shugaban kasa a 2019.

‘Dan takarar Shugaban kasar na PDP ya bayyana haka ne lokacin da ya zanta da ‘Ya ‘yan Jam’iyyar a Garin Jos a Jihar Filato inda yake neman su mara masa baya wajen ganin ya samu tikitin PDP a zaben fitar da gwani nan gaba.

KU KARANTA: Ina da Digiri sama da 10 don haka ni na dace in rike Najeriya – Dankwambo

Gwamnan na Gombe yake cewa idan har ya zama Shugaban kasa, ilmi zai zama kyauta a Najeriya kamar yadda su ka yi karatu ba tare da biyan ko sisi ba a zamanin su. ‘Dankwambo yace zai so yayi wa ‘Yan Najeriya abin da aka yi masa a baya.

Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo ya dai yi alkawari a baya cewa zai ga karshen kashe-kashen da ake yi a Najeriya da sunan addini ko wata kabila idan har ya samu darewa kan karagar mulki a karkashin babbar Jam’iyyar adawar ta PDP a 2019.

‘Dan takaran na 2019 ya kuma bayyanawa ‘Yan PDP irin gogewar sa a harkar Boko inda yayi Digiri rututu da kuma sanin aikin Gwamnatin sa bayan ya rike mukamin akanta Janar na kasar nan sannan kuma yayi Gwamna na tsawon shekaru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel