Daurin shekaru 100: Shugaba Buhari ya shirya yafewa wani barawon gwamna

Daurin shekaru 100: Shugaba Buhari ya shirya yafewa wani barawon gwamna

- Buhari zai yi wa daya daga cikin barayin Najeriya da aka daure shekara 100 afuwa

- Sunan tsohon gwamnan Ambrose Alli

- Ya kuma yi gwamnan tsohuwar jihar Bendel

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya shirya tsaf tomin yafewa wani tsohon gwamnan tsohuwar jihar Bendel yanzu kuma jahohin Edo da Delta a Najeriya, Farfesa Ambrose Alli da aka zarga da hadame kudaden al'ummar jihar.

Daurin shekaru 100: Shugaba Buhari ya shirya yafewa wani barawon gwamna

Daurin shekaru 100: Shugaba Buhari ya shirya yafewa wani barawon gwamna
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a jam'iyyar PDP ta kasa

Mun samu cewa a lokacin mulkin shugaba Buhari na farko yana soja a shekarar 1983, wata kotu ta yankewa tsohon gwamnan wanda tuni ya mutu hukuncin dauri a gidan yari na shekaru 100 saboda samun sa da laifin karkatar da kudin yin wata hanya.

Legit.ng ta samu sai dai gwamnan jihar Edo a yanzu, Mista Godwin Obaseki ya bayyana cewa sun yi magana da shugaban kasa game da yi masa afuwa kuma shugaban ya bayar da tabbacin yin hakan kamar yadda ya bukata.

Gwamnan dai ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron tunawa da shi da aka gudanar a garin Benin, babban birnin jihar ta Edo.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Kano mun samu cewa sun kai wata mamaya a gidan shugaban kwamitin riko na jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kano ranar Litinin din da ta gabata, 24 ga watan Satumba.

Su dai 'yan sandan kamar yadda muka samu, sun je gidan shugaban rikon ne dake a kan titin Sokoto dake garin na Kano inda suka tarwatsa 'ya'yan kwamitin da sauran magoya bayan jam'iyyar ta PDP a jihar Kano dake shirin gudanar da wani taro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel