Ban yi danasanin garkuwa da dan shugaban APC ba – Mai laifi

Ban yi danasanin garkuwa da dan shugaban APC ba – Mai laifi

Wata mata mai garkuwa da mutane, Fatima Muhammad, yayinda yan sanda suka gurfanar da ita a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba tace ba ta yi danasanin sace yaron Bukar Dalori, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress mai shekaru hudu da tayi ba.

Fatima tayi Magana a ranar Litinin lokacin da aka gurfanar da ita jim kadan bayan an kama ta a Maiduguri.

“Na aikata laifin ne saboda ina son kudi. Ba na danasanin akan laifin da na aikata kuma koda ace dan cikina ne, zan sace shi do kudi.

“Na san cewa dan shugaban APC ne; na dauke shi ne saboda ina bukatar kudin da zan wataya a wani waje. Ta yaya zanyi danasanin komai?” inji Fatima.

Ban yi danasanin garkuwa da dan shugaban APC ba – Mai laifi

Ban yi danasanin garkuwa da dan shugaban APC ba – Mai laifi
Source: UGC

Da farko, kwamishinan yan sanda, Damian Chukwu yace Fatima ta haihu da namiji kwanan nan lokacin da aka kama ta a Albarka Hotel dake Maiduguri a ranar 21 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Mambobin APC da PDP sun kara gabannin sake zaben Osun

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Fatima ta sace yaron tare da wasu biyu daga makaranta sannan ta nemi kudin fansa naira miliyan 20.

Ban yi danasanin garkuwa da dan shugaban APC ba – Mai laifi

Ban yi danasanin garkuwa da dan shugaban APC ba – Mai laifi
Source: UGC

Chukwu yace matar da wadanda abun ya shafa na cikin kyakyawar yanayi a lokacin da aka kama ta.

Kwamishinan yace an kama wasu mutane biyu kuma, Muhammed Musa da Muktar Ali-Shaibu, dukkansu daga yankin Bulumkutu dake Maiduguri, a Kano a lokacin da zasu karbi kudin fansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel