APC ba za ta taba bai wa masu son zuciya dama ba irin Saraki da Dogara - Oshiomhole

APC ba za ta taba bai wa masu son zuciya dama ba irin Saraki da Dogara - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya sha alwashin cewa jam'iyyar ba za ta taba bayar da dama ba ta madafa kofa bude a karkashin inuwar ta ga wasu 'yan siyasa domin cimma manufofinsu na soyuwar zukata.

Kwamared Oshiomhole ya bayyana cewa, tuni aka yi walkiya kuma suka farga ta fuskar daukan izina dangane da kura-kuren da jam'iyyar ta tafka a baya, inda ya ce a shirye take wajen tsarkake ta daga bai wa miyagun 'yan siyasa tikitinta na takara a yayin babban zabe na 2019.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Oshiomhole ya bayyana hakan ne a yayin tantance manema takarar kujerun Gwamna da kuma na majalisar dokoki ta tarayya cikin babban birnin kasar nan na Abuja a ranar Litinin din da ta gabata.

APC ba za ta taba bai wa masu son zuciya dama ba irin Saraki da Dogara - Oshiomhole

APC ba za ta taba bai wa masu son zuciya dama ba irin Saraki da Dogara - Oshiomhole
Source: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa, duk da cewar shugaban jam'iyyar bai zayyana sunayen shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da kuma na majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya yi jirwaye mai kama da wanka dangane da ababen da suka aikata.

Ya ke cewa, duk wata barazana da kalubale da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu ya bayu ne a bisa rawar da shugabannin majalisar tarayya suka taka musamman da manufa ta cimma burikan su na son zuciya.

KARANTA KUMA: 2019: A jihar Kwara kadai Saraki zai samu shiga - Sanata Ndume

Oshiomhole ya hikaito yadda majalisar ta tarayya ta kawo tangarda wajen shigar da kasafin kasar nan na 2018 cikin doka, ta hanyar kawo tsaiko ba tare da wata hujja ko ta sisin kobo domin cimma manufa ta karan kansu da a halin yanzu wannan lamari ke barazana ga tattalin arzikin kasa.

Shugaban jam'iyyar ya kuma bayyana takaicinsa na damuwa dangane da yadda majalisar ke ci gaba da kawo tsaikon sanya kasafin hukumar zabe ta INEC da za ta kammala duk wani shiri na zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel