Mambobin APC da PDP sun kara gabannin sake zaben Osun

Mambobin APC da PDP sun kara gabannin sake zaben Osun

Rahotanni sun kawo cewa an kara tsakanin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da na Peoples Democratic Party (PDP) kan zargin wani yunkuri da yan siyasa suka yin a siyan katin zabe gabannin zaben gwamna da za’a sake gudanarwa a wasu kananan hukumomin jihar Osun a ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa rikicin ya barke ne bayan wani jigon PDP, Fatai Oyedele, wanda aka fi sani da Diekola ya jagoranci wasu shugabannin jam’iyyar zuwa mazaba ta 17 a ward 5 a Alekuwodo kan zargin siyan katin zabe.

An tattaro cewa yan sanda sun kama jigon na PDP kan zargin haka, amma jam’iyyar tan ace kan cewa yana kamfen don samun kuri’u ne ba wai siyan katin zabe ba kamar yadda ake zargi.

Mambobin APC da PDP sun kara gabannin sake zaben Osun

Mambobin APC da PDP sun kara gabannin sake zaben Osun
Source: UGC

Wani idon shaida ya fada ma jaridar cewa wakilai da shugabannin APC da na PDP sun zo ward 5, mazaba na 17 dake Alekuwodo domin zawarcin masu jefa kuri’u kafin rikicin ya barke.

Sai dai, kakakin APC a jihar Osun, Kunle Oyatomi, yayi gagawar karyata cewar magoya bayan jam’iyyar sun kasance cikin rikicin. Yayi ikirarin cewa an kama jigon PDP, Oyedele dauke da katin zabe 62.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Jami’an tsaro sun kama shugabannin jam’iyyar PDP a Osun

A nashi bangaren, daraktan labarai na kungiyar kamfen din Adeleke, dan takarar PDP, Olawale Rasheed yayi zargin cewa Oyedele na nemawa PDP magoya baya ne a yankin da za’a sake zabe lokacin da yan iskan PDP suka kai masa hari.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa ba’a tabbatar da lamarin daga wajen yan sanda ba saboda wayar kakakin yan sandan jihar Osun, Folashade Odoro ya kasance a kashe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel