Babbar magana: FRSC ta tantance mutane 300,000 da ke neman aikin mutane 4,000 a hukumar

Babbar magana: FRSC ta tantance mutane 300,000 da ke neman aikin mutane 4,000 a hukumar

- FRSC ta soma tantance mutane 324,000 da ke neman gurbin aikin mutane 4,000 a hukumar

- Cibiyoyin da ake tantancewar sun hada da barikin soji na Sani Abacha da ke Asokoro, da kuma babban filin wasanni na kasa da ke Abuja

- Tantancewar da aka fara a ranar Litin, ana sa ran kammalawa a ranar Asabar, 29 ga watan Satumba, 2018

Hukumar kiyaye hadurra da lafiyar tituna ta kasa FRSC ta soma daukar aiki tare da tantance lafiyar masu neman aikin, inda ta tantance mutane 324,000 da ke neman gurbin aikin mutane 4,000 da hukumar ta ce ta ke nema.

Corps Marshall Boboye Oyeyemi ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara cibiyoyin tantancewar guda 2 da ke a babban birnin tarayya Abuja, a ranar litin 24 ga watan Satumba, 2018.

Cibiyoyin da ake tantancewar sun hada da barikin soji na Sani Abacha da ke Asokoro, da kuma babban filin wasanni na kasa da ke cikin garin Abuja.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Matasan Niger Delta sun amince Sule Lamido ya zama shugaban kasa karkashin PDP

Kamfanin dillancon labarai na NAN ya ruwaito cewa ana tantancewar ne don daukar aiki a matakai daban daban da suka hada da ofisoshi, Marshal Inspectorates da kuma Road Marshal Assistants.

Babbar magana: FRSC ta fara tantance mutane 300,000 da ke neman aikin mutane 4,000 a hukumar

Babbar magana: FRSC ta fara tantance mutane 300,000 da ke neman aikin mutane 4,000 a hukumar
Source: Depositphotos

Oyeyemi ya ce: "Muna kan tantance akalla mutane 324,000 da suka zo daga fadin kasar, cikinsu akwai mutane 105,000 da suka kammala karatun degree."

Ya ce duka duka wadanda za a dauka aiki a karkashen tantancewar, ba za su haura mutane 4,000 ba.

"Daga ciki mutane 4,000 da zamu dauka, 400 ofisoshi ne, 1,000 kuwa na Sifeta Marshal ne, sai kuma Road Marshal Assistants guda 3,200. Duba da yawan masu bukatar aikin, wannan ne ya sa tilas muka baiwa JAMB damar gudanar da jarabawar shiga aikin.

"Bayan sun kammala jarabawar, sannan sai suje a yi masu gwaji ko suna tu'ammali da muggan kwayoyi; daga karshe kuma sai su fuskanci tantancewar karshe daga Corps Marshal," a cewar Oyeyemi.

Tantancewar da aka fara a ranar Litin, ana sa ran kammalawa a ranar Asabar, 29 ga watan Satumba, 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel