2019: A jihar Kwara kadai Saraki zai samu shiga - Sanata Ndume

2019: A jihar Kwara kadai Saraki zai samu shiga - Sanata Ndume

Mun samu cewa wani Sanatan jihar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yiwa shugaban majlisar dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki wankin babban bargo kan kudiri da aniyar sa ta samun nasara yayin neman kujerar shugaban kasa.

Sanata Ndume ya bayyana wannan kudiri na Saraki tamkar shafa labari shuni ko wata tatsuniya da ba ta da wani tasiri ta fuskar barazana ko kalubale kan kudirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman tazarcen kujerarsa.

A jihar Kwara kadai Saraki zai samu nasarar Zabe - Sanata Ndume

A jihar Kwara kadai Saraki zai samu nasarar Zabe - Sanata Ndume
Source: UGC

Saraki wanda a kwana-kwanan nan ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP ya na kuma ci gaba da fafutika ta neman kujerar shugaban kasa a yayin babban zabe na 2019.

A yayin ganawarsa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan Abuja, Sanata Ndume wanda ba sa ga maciji da Saraki sakamakon raba gari da juna tun a shekarar 2017 da ta gabata ya bayyana cewa, Saraki a jihar Kwara kadai zai iya samun nasarar zabe kasancewar ta mahaifar sa.

KARANTA KUMA: 2019: Ba ni da wani zabi da ya wuce David Mark - Jonathan

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito, Saraki wanda a yayin ci gaba da yawon karade yankunan daban-daban na kasar nan ya ce ba bu mafificin dan takara dake da makamanciyar cancanta irin ta sa ta fuskar jagorancin kasar nan da zai hada kanta wuri guda.

Sai dai a yayin ci gaba da jan Gora ga shugaban majalisar dattawan, Sanata Ndume ya kuma bayyana cewa, a wurin al'ummar yankin Arewa ta Tsakiya ne kadai Saraki zai samu shiga kasancewar yankin ya hadar har da jiharsa ta Kwara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel