Zaben 2019: Matasan Niger Delta sun amince Sule Lamido ya zama shugaban kasa karkashin PDP

Zaben 2019: Matasan Niger Delta sun amince Sule Lamido ya zama shugaban kasa karkashin PDP

- Hadakar kungiyoyin matasan Niger Delta sun amince Sule Lamido ya zama shugaban kasa karkashin PDP

- Matasan sun ce za suyi duk mai yiyuwa don ganin Lamido ya samu nasarar samun tikitin takara a babban zaben fitar da gwani na jam'iyyar

- Sun ce daga 2015 zuwa 2017 Sule Lamido ya taka muhimmiyar rawa ga rayukan jama'a duk da cewa ba PDP ba ce akan mulki

A ci gaba da fuskantar babban zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP, wanda zai gudana a ranar 6 ga watan Oktoba 2018, matasan Niger Delta, karkashin Urhobo, da ke tafiya tare a inuwa kungiyar matasan shiyyar Kudu-maso-kudu don kawo zaman lafiya (SSYPM), sun amince Sule Lamido ya zamo shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mataimakin shugaban kungiyar ta SSYPM, Comrade Godwin Eheriene, wanda ya bayyana tsohon gwamnan jihar Jigawa a matsayin mutum wanda ya yarda da yin adalci ba tare da nuna wariyar shiyya ba.

Dama zuwa hagu: Dr. Rabiu Musa kwankwaso, Dr. Sule Lamido, da Atiku Abubakar

Dama zuwa hagu: Dr. Rabiu Musa kwankwaso, Dr. Sule Lamido, da Atiku Abubakar
Source: Twitter

Erheriene ya ce kungiyar za tayi duk mai yiyuwa don ganin cewa tsohon ministan harkokin kasashen wajen, ya zama dan takarar jam'iyyar PDP don jagorantar jam'iyyar a babban zabe na 2019.

KARANTA WANNAN: Hukumar sojin sama ta bude katafaren dakin binciken laifuka na kimiyya, hotuna

Kadan daga cikin abun da sanarwar ta kunsa: "Kungiyar matasan shiyyar Kudu maso Kudu don kawo zaman lafiya, kungiyar matasan Niger Delta da kuma wasu kungiyoyin fararen hula da ke a yankin Niger Delta, sun amince da yin kira ta bakin shugaban hadakar kungiyoyin Comrade Godwin Erheriene akan Sule Lamido ya zama dan takarar shugaban kasa karkashin PDP."

Sun yi nuni da cewa a matsayin sule Lamido na dan siyasa, ya bada gagarumar gudunmowa wajen ganin an kare demokaradiyya a kasar da kuma tabbatar da yiwa kowacce shiyya adalci, duk da cewa ba PDP ba ce ke mulki daga 2015 zuwa 2017.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel