Adawa da tazarcen Buhari: Mutumin da ya fara tattaki daga Legas ya iso Abuja, hotuna

Adawa da tazarcen Buhari: Mutumin da ya fara tattaki daga Legas ya iso Abuja, hotuna

Wani mutum, Isa Mohammed, da fara tattaki daga jihar Legas a kwanakin baya, saboda nuna adawar sa da sake tsayawar Buhari takarar shugaban kasa, ya iso Abuja da yammacin yau, Litinin.

Wannan ba shine karo na farko da wani matashi ya yi tattaki zuwa Abuja saboda Buhari ba. Sai dai ragowar da suka yi tattaki zuwa Abuja, sun yi ne saboda kaunar shugaba Buhari.

A shekarar 2015, bayan shugaba Buhari ya ci zaben shugaban kasa, wasu matasa biyu; daya daga Legas, daya kuma daga Yola, sun yi tattaki zuwa Abuja domin murnar cin zaben Buhari a lokacin.

Adawa da tazarcen Buhari: Mutumin da ya fara tattaki daga Legas ya iso Abuja, hotuna

Isah Mohammed bayan ya ya iso Abuja
Source: Facebook

Adawa da tazarcen Buhari: Mutumin da ya fara tattaki daga Legas ya iso Abuja, hotuna

Isah bayan ya bar Legas
Source: Facebook

Shi dai matashin na da ra'ayin cewar kuskure ne shugaba Buhari ya nemi tazarce saboda tsananin rayuwa da yace 'yan Najeriya na fuskanta sakamakon matakin tsauri da Buharin ya dauka a bangaren tattalin arzikin kasa.

DUBA WANNAN: Zaben Osun: PDP ta garzaya kotu da wasu bukatu 2

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar majalisar tarayyar Najeriya; majalisar wakilai da ta dattijai, ta bayyana cewar ba zata dawo daga hutun da ta tafi a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, ba tare da bayyana ranar 9 ga watan Oktoba a matsayin ranar da suka matsar da dawowar ta su.

Wannan sanarwa na kunshe cikin sanarwar da magatakardar majalisa ya aike ga mambobin majalisar wakilai da ta dattijai a jiya, Lahadi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel