Kwankwaso ya fadi kuskuren da Shugaba Buhari yayi a mulki a 2015

Kwankwaso ya fadi kuskuren da Shugaba Buhari yayi a mulki a 2015

Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana kuskuren da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bayan ya samu mulkin Kasar nan a 2015.

Kwankwaso ya fadi kuskuren da Shugaba Buhari yayi a mulki a 2015

Kwankwaso yace Buhari yayi kuskure wajen kin nade Ministoci da wuri
Source: Depositphotos

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana a gidan Talabijin na Channels a Garin Legas makon jiya inda ya tattauna kan batutuwa da dama da su ka shafi harkar siyasar kasar nan. Kwankwaso yace Buhari yayi nawa wajen nada Ministocin sa.

'Dan takarar Shugaban kasan na Jam'iyyar PDP ya nuna cewa bata lokacin da Shugaban kasa Buhari yayi wajen kafa Gwamnati a 2015 ne ya jawo Najeriya ta samu kan ta cikin matsalar tattalin arziki. Buhari yayi kusan watanni 6 kafin ya samu Ministoci.

KU KARANTA: Abin da na ke da shi da su Kwankwaso ba su da shi – Ahmed Makarfi

Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa bayan ya sake zama Gwamna karo-na-biyu a 2011, a makon farko ya aika sunayen Kwamishinonin sa zuwa Majalisar dokokin Kano kuma kafin aje ko ina ya fara aiki tukuru har zuwa Ranar da ya sauka daga mulki.

A hirar dai 'Dan siyasar ya bayyana cewa Gwamnantin nan ta nuna cewa ba za ta iya rike kasar nan ba. Kwankwaso yace idan PDP ta ba sa tikiti a 2019, Jam'iyyar ta samu wanda zai iya doke Shugaban kasa Buhari sannan kuma yayi aikin da ya kamata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel