Da duminsa: Jami’an tsaro sun kama shugabannin jam’iyyar PDP a Osun

Da duminsa: Jami’an tsaro sun kama shugabannin jam’iyyar PDP a Osun

Da yammacin yau, Litinin, ne jam’iyyar adawa ta PDP tayi zargin cewar jami’an tsaro na kama shugabanninta a garuruwan Osogbo, Ile Ife da Orlu – garuruwan da za a sake maimaita zabe ranar Alhamis.

A sakon da PDP ta saki a shafinta na Tuwita ta ce an kama wani jigo a jam’iyyar , Alhaji Fatal Diekola, a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

An kama Alhaji Fatal Diekola, daya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar PDP a Osogbo. An yi masa duka tare da korar hadimansa duk da halin rashin koshin lafiya da yake ciki. Ragowar mambobin mu a Osogbo na jin tsoron kwana a gidajensu saboda cigaba da muzguna masu da jami’an tsaro ke yi,” a cewar uwar jam’iyyar PDP.

Da duminsa: Jami’an tsaro sun kama shugabannin jam’iyyar PDP a Osun

Dan takarar jam’iyyar PDP a Osun; Sanata Ademola Adeleke
Source: Twitter

Kazalika PDP ta bayyana cewar haka lamarin yake a karamar hukumar Orolu, inda ta zargi ‘yan bangar APC da kaiwa shugabanninta hari da safiyar yau, Litinin.

DUBA WANNAN: APC ta kori mataimakin bulaliyar majalisar wakilai daga jam'iyyar

A jiya, Lahadi, ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da cewar akwai bukatar yin zaben kece raini a tsakanin dan takarar jam’iyyar APC, Isiaka Gboyega, da na jam’iyyar PDP, sanata Ademola Adeleke, bayan ‘yan takarar biyu sun kusan yin kunnen doki a zaben gwamnan jihar Osun da aka yi ranar Asabar da ta wuce.

A yau ne dai masoyan dan takarar PDP, Sanata Ademola Adeleke, da magoya bayan jam'iyyar suka gudanar da zanga-zanga a shelkwatar INEC dake Osogbo domin nuna rashin amincewarsu da matakin da INEC din ta dauka a kan zaben jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel