APC ta kori mataimakin bulaliyar majalisar wakilai daga jam'iyyar

APC ta kori mataimakin bulaliyar majalisar wakilai daga jam'iyyar

Jam'iyyar APC ta kori mataimakin bulaliyar majalisar wakilai, Mista Pally Iriase, bisa zarginsa da cin dunduniyar jam'iyya.

Rahotanni sun bayyana cewar shugabancin APC a mazabar dan majalisar ne ya fara sanar da korar dan majalisar kafin daga bisani shugabancin karamar hukumar Owan, da yake wakilta, ta bayyana amincewar ta da hukuncin shugabancin mazabar Mista Iriase.

Takarar korar da jam'iyyar APC ta nunawa manema labarai na dauke da sa hannun Zuberu Shabah, shugaban APC na karamar hukumar Owan, da sakatarensa, Theophilus Aigboje.

APC ta bayyana cewar ta kori dan majalisar ne saboda cin dunduniyar jam'iyyar da yake yi ta hanyar umartar magoya bayansa su koma PDP tare da tsayar da babban hadiminsa takara a jam'iyyar, da kuma daina halartar duk wani taro na APC.

APC ta kori mataimakin bulaliyar majalisar wakilai daga jam'iyyar

majalisar wakilai
Source: UGC

Tuni dai shugabannin APC na karamar hukumar Owan suka aike ta takardar korar Mista Iriase ga shugabancin jiha domin mika ta ga shugabancin jam'iyyar na kasa. Shugabannin sun bayyana cewar sun bi dukkan dokokin kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC kafin korar Mista Iriase.

DUBA WANNAN: Dalilai 5 da suka sa APC ta kasa lashe zaben jihar kamar yadda ta lashe na jihar Ekiti

Yayin hutun karshen mako ne kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito Mista Iriase na cewar yana fuskantar matsin lamba a kan sai ya koma PDP.

Duk kokarin jin ta bakin dan majalisar a kan korar da APC tayi masa bai yiwu ba saboda duk layukan wayarsa a kashe suke lokacin da jaridar Vanguard ta tuntube shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel