Yanzu Yanzu: Daruruwan magoya bayan PDP sun yi zanga-zanga a hedkwatar INEC dake Osun

Yanzu Yanzu: Daruruwan magoya bayan PDP sun yi zanga-zanga a hedkwatar INEC dake Osun

Daruruwan magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba sun mamaye hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta dake Osun don yin zanga-zanga akan sake zaben gwamna a jihar da hukumar tayi umurni.

Masu zanga zangar sun kasance da kwalayen sanarwa da rubutu daban-daban kasar “Babu sake zabe, “INEC kada ku hada kai da APC”; “Mutane sun yi Magana a ranar Asabar, ku sanar da sakamakon zabe” da dai sauransu.

Masu zanga-zangar su caccakin hukumar INEC kan kin kaddamar da Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara a zaben baya ya samu adadin kuri’u mafi yawa.

Yanzu Yanzu: Daruruwan magoya bayan PDP sun mamaye hedkwaar INEC

Yanzu Yanzu: Daruruwan magoya bayan PDP sun mamaye hedkwaar INEC
Source: Original

Sun ce mutanen jihar sun yi Magana kuma maf yawancin masu zaben sun so Adeleke a matsayin gwamnan jihar sannan kuma cewa ya kamata a mutuntaburin mutanen.

KU KARANTA KUMA: APC ta sanya jigonta a kwana kan halartan gangamin PDP da yayi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani dan takarar kujeran gwamna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Mohammed Abba-Aji ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) saboda tsarin zaren fidda gwani na wakilai da jam’iyyar ta zabi yi a jihar.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa a yanzu Abba-Aji na neman takarar kujeran sanata na Borno ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP. Dan siyasan yace matsalolin cikin gida dake damun APC a jihar ne ya sanya shi ficewa daga jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel