Dan takaran SDP da ya samu kuri'u 128,049 ya amince da hadin kai da PDP domin kada APC ranan Alhamis - Saraki

Dan takaran SDP da ya samu kuri'u 128,049 ya amince da hadin kai da PDP domin kada APC ranan Alhamis - Saraki

Shugaban majalisar dattawa, kuma shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Osun a jam’iyyar PDP, Bukola Saraki, ya bayyana cewa dan takaran SDP da ya samu kuri'u 128,049 ya amince da hadin kai da PDP domin kada APC.

Sanatan wanda tsohon dan jam’iyyar PDP ne kuma ya taka rawan gani a zaben yarda zasu hada karfi da karfe wajen kayar da APC a karashen zaben da za’a yi ranan Alhamis, 27 ga wtaan Satumba 2018.

Saraki ya bayyana hakan ne bayan ganawar da yayi da Omisore a garin Ile-Ife.

Yace: “Na godewa Sanata Iyiola Omisore da irin kyakkyawan tarban da suka yi min da tawaga na a Ile-Ife yai. Mun yi yarjejeniyan aiki tare saboda duk daya muke.”

Dan takaran SDP da ya samu kuri'u 128,049 ya amince da hadin kai da PDP domin kada APC ranan Alhamis - Saraki

Dan takaran SDP da ya samu kuri'u 128,049 ya amince da hadin kai da PDP domin kada APC ranan Alhamis - Saraki
Source: Twitter

KU KARANTA: APC ta sanya jigonta a kwana kan halartan gangamin PDP da yayi

Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 254,699; Gboyegaa Oyetola na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 254, 345, sannan Sanata Iyiola Omisore na jam’iyyar SDP ya samu kuri’u 128, 049.

Hukumar INEC tace ba zai yiwu ta alanta dan takaran jam’iyyar PDP a matsayin zakaran zaben ba saboda tazarar da ya baiwa mai binsa bai kai yawan kuri’un da akayi wasti da sub a, saboda haka sai an sake gudanar da wani zabe a wuraren da aka samu matsala.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel