Zan marawa duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP baya – Sanata Mark

Zan marawa duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP baya – Sanata Mark

Dan takarar kujeran shugaban kasa a PDP kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, yace zai marawa duk dan takarar da yayi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda za’a gudanar a garin Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

Mark ya bayyana hakan a ranar Litinin, 4 ga watan Satumba a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa.

Ya kuma nemi goyon bayan mambobin jam’iyyar sannan ya bukaci da su zabe shi a lokacin zaben fidda gwani domin bashi damar samun tikitin takara a 2019.

Zan marawa duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP baya – Sanata Mark

Zan marawa duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP baya – Sanata Mark
Source: Depositphotos

Yace: "Zamu yi fafutuka sannan mu kwato mulki daga hannun jam’iyyar Progressives People Congress (APC)."

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani dan takarar kujeran gwamna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Mohammed Abba-Aji ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) saboda tsarin zaren fidda gwani na wakilai da jam’iyyar ta zabi yi a jihar.

KU KARANTA KUMA: APC ta sanya jigonta a kwana kan halartan gangamin PDP da yayi

Jaridar This Day ta ruwaito cewa a yanzu Abba-Aji na neman takarar kujeran sanata na Borno ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP.

Dan siyasan yace matsalolin cikin gida dake damun APC a jihar ne ya sanya shi ficewa daga jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel