2019: Jihar Kwara kadai Saraki zai iya kawowa – Sanata Ndume

2019: Jihar Kwara kadai Saraki zai iya kawowa – Sanata Ndume

Wani mamba a majalisar dokokin kasar, Sanata Ali Ndume ya yi watsi da kudri takarar shugaban kasa na shugaban majalisar dattawa,Bukola Saraki, inda ya bayyana hakan a matsayin mafarki, sannan cewa hakan ba zai zamo barazana ga tazarcen Buhari ba.

Saraki wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa babban jam’iyyar adawa ta PDP a kwanakin baya na son zama shugaban kasar na gaba a zaben 2019.

Da yake hira da kamfanin dillancin labaran Najeriyaa a Abuja, Ndume wanda ya kasance na kua da shgaban majalisar dattawa kafin su raba garia 2017, ya bayyana cewa Saraki zai iyakawo jiharsa ta Kwara ne kadai.

2019: Jihar Kwara kadai Saraki zai iya kawowa – Sanata Ndume

2019: Jihar Kwara kadai Saraki zai iya kawowa – Sanata Ndume
Source: UGC

Yace yan Najeriya ba zasu zabe shi ba sai dai yan jihar Kwara kadai. Cewa ta yaya mutumin da ya kasa rike majalisar dattawa kadai zai iya rike kasar Najeriya baki daya.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar kujeran gwamna na PDP a zaben 2015 ya sauya sheka zuwa APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Dan takarar kujeran shugaban kasa a PDP kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, yace zai marawa duk dan takarar da yayi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda za’a gudanar a garin Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

Mark ya bayyana hakan a ranar Litinin, 4 ga watan Satumba a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa.

Ya kuma nemi goyon bayan mambobin jam’iyyar sannan ya bukaci da su zabe shi a lokacin zaben fidda gwani domin bashi damar samun tikitin takara a 2019.d

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel