Gwamnatin tarayya ta canjawa wasu manyan sakatarori 4 wurin aiki

Gwamnatin tarayya ta canjawa wasu manyan sakatarori 4 wurin aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da yiwa wasu famanen sakatarorin gwamnatin tarayya canjin wuraren ayyukansu kamar yadda shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Winifred Oyo-Ita ta sanar a yau Litinin a Abuja.

Ta ce an dauke Mu'azu Abdulkadir daga Hukumar Tarayya ta Karafa da Hakar Ma'adinai zuwa Hukumar Ayyukan Gona da Raya Karkara.

Gwamnatin tarayya ta canjawa wasu manyan sakatarori 4 wurin aiki

Gwamnatin tarayya ta canjawa wasu manyan sakatarori 4 wurin aiki
Source: Twitter

"Mrs Georgina Ehuria, Babban Sakatariyar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya yanzu ta koma Hukumar Hukumar Tarayya ta Karafa da Hakar Ma'adinai.

DUBA WANNAN: Ina satar baburan mutane duk lokacin da na bukaci kudin kashewa - Gimba

"Babban Sakataren Ayyuka na Musamman na ofishin Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya Mr Aliboh shi kuma ya koma Ma'aikata Muhalli na Kasa.

" Alhaji Suleiman Mustapha na ofishin Kula da ayyuka na ofishin shugaban ma'aikatan tarayya na kasa ya koma Ma'aikatar Ayyukan Kasashen Ketare."

Shugaban ma'ikatan gwamnatin tarayyar ta bukaci a kammala musayar takardun wuraren ayyukan kafin ranar 29 ga watan Satumban shekarar 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel