Da dumi-dumi: PDP ta fara tantance 'yan takarar shugaban kasa

Da dumi-dumi: PDP ta fara tantance 'yan takarar shugaban kasa

Mun samu daga Punch cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta fara tantance masu neman takarar shugabancin kasa na jam'iyyar.

'Yan takarar dai sune wadanda suka saya fom din neman takarar kuma za su fafata a zaben fidda gwani da jam'iyyar za ta gudanar a ranakun 5 da 6 na watan Oktoba a Fatakwal da ke jihar Rivers.

A halin yanzu dai ana can ana tantance 'yan takarar a ofishin kamfe na jam'iyyar mai suna Legacy House da ke Maitama Abuja inda kwamitin tantancewar karkashin jagorancin Namadi Sambo ta ke tantance 'yan takarar.

Yanzu-yanzu: An fara tantance masu neman takarar shugabancin kasa a PDP

Yanzu-yanzu: An fara tantance masu neman takarar shugabancin kasa a PDP
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Atiku ya bayyana sababbin rikicin makiyaya da manoma a Benue

'Yan takarar da suka halarci wajen tantancewar sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.

Sauran su ne tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmad Makarfi da ma wasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel