Dan takarar kujeran gwamna na PDP a zaben 2015 ya sauya sheka zuwa APC

Dan takarar kujeran gwamna na PDP a zaben 2015 ya sauya sheka zuwa APC

Dan takarar kujeran gwamna a karkashin jam’iyyar PDP, a jihar Borno a zaben 2015, Gambo Lawan, ya bar jam’iyyarsa inda ya koma jam’iyyar APC yayinda ya shiga daga masu neman tikitin jam'iyyar a zaben 2019.

Mista Lawan, tsohon shugaban matatar mai dake Warri, bai yi nasara ba akan gwamna mai ci, Kashim Shettima, a lokacin zaben 2015.

A lokacin da yayi takara karkashin PDP a zaben 2015, mista Lawan ya samu kuri’u 34,731 amman gwamna mai ci ne yayi nasara inda ya samu kuri’u 649,913.

Ya daura laifin rashin nasaransa kan tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, wanda yace ya hada baki da tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ali Sheriff, wajen hana shi tikitin da ya lashe a zaben fidda gwani.

Dan takarar kujeran gwamna na PDP a zaben 2015 ya sauya sheka zuwa APC

Dan takarar kujeran gwamna na PDP a zaben 2015 ya sauya sheka zuwa APC
Source: UGC

Wata babban kotun Abuja ce ta kwato wa Mista Lawal tikitinsa.

Kuna iya tunawa a baya cewa jam’iyyar PDP a Borno ta canja dan takarar gwamna, Muhammed Imam, mako daya kafin zaben gwamna a 2015, inda aka maye gurbi shi da Mista Lawan, wanda babban kotun Abuja ta bayyana a matsayin wanda ya lashe fidda gwani na jam'iyyar.

Mista Lawan yace ya share kimanin watanni hudu da ya kamata ace yayi amfani dasu wajen yakin neman zabe wajen kwato tikitinsa da aka sata, “wannan ne sanadiyan rashin samun isasshen lokaci na yakin neman zabe na”.

KU KARANTA KUMA: 2019: Wani mutum mai suna Jonathan ya bayar da mota guda da ya mallaka ga Atiku

Tattare da bacin ransa akan rawar ganin da tsohuwar jam’iyyarsa ta taka a 2015, Mista Lawan yace ya zabi shiga APC inda yake ganin zai cimma burinsa na zama gwamna mai jiran gado.

Yayinda yake magana da manema labarai jim kadan bayan ya mayar da fam dinsa na takarar a sakaterian APC na jihar, Mista Lawan yace yunkurinsa na zama gwamnan jihar Borno ba don komai bane illa mayar ma al’umma “alkhairi da suka nuna mishi”.

Ya kara da cewa ya shiga jam’iyyar APC ne saboda matsayin shugaban kasa Muhammadu Buhari na “Mutum mai gaskiya wanda ke tsayawa akan gaskiya”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel