APC ta sanya jigonta a kwana kan halartan gangamin PDP da yayi

APC ta sanya jigonta a kwana kan halartan gangamin PDP da yayi

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na tuhumar wani jigonta tsohon jakada Yahaya Kwande, wanda ya kasance jigo a kwamitin amintattu na jam’iyyar.

Letep Dabang, shugaban APC na jihar Plateau, wanda ya sanya hannu a tuhumar da ake masa ya bayyana cewa Kwande, tsohon jakada a Switzerland ya halarci gangamin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jos harma yayi Magana a taron.

Dabang ya bukaci Kwande da ya mayar da martan ga jam’iyyar ta hannunsa cikin sa’o’i 24 ko kuma ya fuskanci hukunci. “Hakan ya munana a matsayinka na dan APC ka halarci gangamin PDP, harma kayi Magana a taron.

“Kamar hakan ai ishe ka ba har ma ga fadama mutane cewa kada suyi mamaki idan ka kawo gwamnan jihar Plateau PDP.

APC ta sanya jigonta a kwana kan halartan gangamin PDP da yayi

APC ta sanya jigonta a kwana kan halartan gangamin PDP da yayi
Source: Depositphotos

“Ka san cewa gwamnan shine shugaban APC a Plateau sannan abunda kayi ya sabama ka’idar jam’iyya sannan hakan babban tozarci ne ga APC,” cewar tuhumar.

Dabang ya bayyana cewa idan har yaki amsa wasikar tuhumar cikin sa’o’i 24 hakan zai iya kai ga dakatar a si sannan kuma a kafa kwamitin da zata yi duba cikin lamarin.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ba zata ji kunyar korarsa ba idan har kwamitin ta bayar da shawarar aikata hakan.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani dan takarar kujeran gwamna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Mohammed Abba-Aji ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) saboda tsarin zaren fidda gwani na wakilai da jam’iyyar ta zabi yi a jihar.

KU KARANTA KUMA: Shugaban karamar hukuma ya tsallake rijiya da baya yayinda yan fashi suka sace mutane 7 a Zamfara

Jaridar This Day ta ruwaito cewa a yanzu Abba-Aji na neman takarar kujeran sanata na Borno ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP.

Dan siyasan yace matsalolin cikin gida dake damun APC a jihar ne ya sanya shi ficewa daga jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel