Manyan dalilai 2 da yasa Saraki ya daga ranan dawowan yan majalisa

Manyan dalilai 2 da yasa Saraki ya daga ranan dawowan yan majalisa

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa majalisar tarayyar Najeriya; majalisar wakilai da ta dattijai, ta bayyana cewar ba zata dawo daga hutun da ta tafi a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, ba tare da bayyana ranar 9 ga watan Oktoba a matsayin ranar da suka matsar da dawowar ta su.

Wannan sanarwa na kunshe cikin sanarwar da magatakardar majalisa ya aike ga mambobin majalisar wakilai da ta dattijai a yau, Lahadi.

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun bayyana manyan dalilai biyu da hana Saraki tsayar da ranan dawowa majalisa gobe Talata:

1. Tsoron kada a tsigeshi da Yakubu Dogara

Kamar yadda ya bayyana, jam’iyyar All Progressives Congress APC ta lashi takobin cewa ko ta kaka sai ta tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da Kakakin majalisar wakilai,Yakubu Dogara daga kujerarsu sakamakon sauya shekarsu da daga jam’iyyar zuwa PDP.

Jam’iyyar ta lashi takobin cewa ba zai yiwu yan jam’iyyar maras rinjaye su jagoranci majalisa ba. Tun lokacin Saraki ya ki dawo da yan majalisa duk da cewan akwai bukatan su dawo domin baiwa hukumar gudanar da zabe ta kasa wato INEC daman fara shirye-shiryen zaben 2019.

KU KARANTA: Buhari ya isa kasar Amurka

2. Sauraron sakamakon zaben fitar da gwanin jam’iyyu

Yayinda dukkan jamiyyun siyasa suka sanya zaben fitar gwanayensu a karshen watan Satumba, Saraki na sauraron ganin ko zai lashe zaben takarar kujeran shugaban kasa da yake nema, amma idan bai samu ba, sai ya sake daura damara domin komawa kujerarsa na majalisa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel