2019: Wani mutum mai suna Jonathan ya bayar da mota guda da ya mallaka ga Atiku

2019: Wani mutum mai suna Jonathan ya bayar da mota guda da ya mallaka ga Atiku

- wani dan Najeriya mai suna Jonathan ya nuna goyon bayansa ga dan takarar kujeran shugaban kasa, Atiku Abubakar

- Ya bayar da mota guda da ya mallaka ga Atiku

- Tsohon mataimakin shugaban kasar ne a shafinsa na twitter

Yayinda zaben 2019 ke kara gabatowa, wani dan Najeriya mai suna Jonathan ya nuna goyon bayansa ga dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Legit.ng ta tattaro cewa Jonathan ya zuba jari a yankin neman zabe Atiku ta hanyar bayar da mota guda daya tal da ya mallaka.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ne ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a ranar Asabar, 2 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Manyan dalilai 2 da yasa Saraki ya daga ranan dawowan yan majalisa

Ya wallafa a shafinsa na twitter cewa: “Yanzun nan Jonathan ya zuba jari a yakin neman zabe na da babban kadarar day a mallaka – mota guda da ya mallaka. Kamar matasan Najeriya da dama, imani da Jonathan yayi dani ba zai tafi a banza ba, sannan wannan ne dalilin da yasa na jajirce wajen ganin na samar da shugabancin da ake bukata domin sake farfado da Najeriya. Nagode Jonathan. "

Ga yanda ya wallafa:

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel