Osun: PDP zasu kulla yarjejeniya tare da Omisore da sauran yan takarar kujeran gwamna

Osun: PDP zasu kulla yarjejeniya tare da Omisore da sauran yan takarar kujeran gwamna

Alamu sun nuna a Abuja a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba cewa shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party na iya kulla yarjejeniya da tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore a kokarinsu na son lashe zaben gwamna a jihar wanda za’a sake gudanarwa a ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.

Omisore ya kasance dan takarar gwamna a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben wanda dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke ya zo na farko da kuri’u 254, 698, yayinda dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mista Gboyega Oyetola, ya zo na biyu da kuri’u 254,345.

Hukumar zabe mai zaman kanta tace za’a sake zabe a wasu mazabu inda aka soke zabuka.

Osun: PDP zasu kulla yarjejeniya tare da Omisore da sauran yan takarar kujeran gwamna

Osun: PDP zasu kulla yarjejeniya tare da Omisore da sauran yan takarar kujeran gwamna
Source: Depositphotos

Mazabun da hukumar ta lissafa guda biyu ne, a karamar hukumar Orolu, daya a karamar hukumar Ife ta kudu, daya kuma a karamar hukumar Ife ta arewa sannan kuma daya a karamar hukumar Osogbo.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsohon hadimin Oshiomhole ya sauya sheka zuwa PDP da dubban magoya bata

An tattaro cewa PDP ta rigada ta fara tattaunawa da Omisore domin ganin tayi nasara a mazaban guda biyu da yafi karfi a Ife.

Baya ga Omisore, PDP na shirin ganawa da yan takarar sauran jam’iyyun siyasa da ake ganin zasu iya tabuka abun azo a gani a lokacin zaben ranar Asabar.

Yan takarar sun hada da na African Democratic Congress’ Fatai Akinbade da kuma na Action Democratic Party’s Alhaji Moshood Adeoti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel